'Kun Shiga Uku': Iran Ta Faɗi Abin da Za Ta Yi Wa Amurka bayan Hari a Cibiyoyin Nukiliyarta

'Kun Shiga Uku': Iran Ta Faɗi Abin da Za Ta Yi Wa Amurka bayan Hari a Cibiyoyin Nukiliyarta

  • Ministan Harkokin Wajen Iran ya gargadi Amurka kan hare-haren da ta kai, yana cewa za su fuskanci ukuba daga kasar
  • Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa an lalata dukkan cibiyoyin nukiliya na Iran yayin da Benjamin Netanyahu ya yaba da matakin da Amurka ta dauka
  • Iran ta bayyana cewa wannan hari wani “shiri ne na tayar da yaki a dukan yankin” kuma tana da dukkan zabin ramawa da take da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Ministan Harkokin Wajen kasar Iran ya yi magana kan harin da Amurka ta kai wa Iran a jiya Asabar.

Abbas Araghchi ya bayyana cewa Amurka “za ta fuskanci bala'i” bayan kai farmaki kan wasu cibiyoyin nukiliya uku na kasar.

Iran ta yi martani bayan harin Amurka a Iran
Iran ta sha alwashin ba Amurka kashi bayan harinta a kasar. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Iran ta sha alwashi bayan harin Amurka

Kara karanta wannan

'Akwai barazana': Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan harin Amurka a Iran

Minista Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan a wata wallafa da ya yi a shafin X jim kadan bayan harin Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya nuna takaici kan lamarin yana mai cewa Tehran na da duk zabin ramawa game da harin.

Harin Amurka, wanda aka aiwatar ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba, ya kai farmaki kan wuraren Fordow, Isfahan da kuma Natanz.

Shugaba Donald Trump ya ce an lalata wadannan wuraren gaba daya yayin da ake cigaba da kai ruwa rana tsakanin kasashen.

A rubutunsa, Ministan harkokin wajen Iran ya ce:

"Amurka, wacce ke daga cikin mambobin dindindin na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ta aikata babban laifi na take dokokin tsarin Majalisar.
"Ta kuma take dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), ta hanyar kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran da ke zaman lafiya.
"Abubuwan da suka faru da safiyar nan abin tir da Allah-wadai ne, kuma za su haifar da mummunan illa mai dorewa.
"Dangane da tanadin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da ke ba da damar kare kai, Iran na da 'yancin daukar duk wani mataki da ya dace domin kare 'yancinta, muradunta da kuma jama'arta."

Kara karanta wannan

Amurka ta kai harin farko Iran, ta jefa bama bamai a manyan wuraren haɗa nukiliya

An soki harin Amurka a kan Iran
Iran ta sha alwashin daukar mataki bayan harin Amurka. Hoto: Getty Images.
Source: Twitter

Benjamin Netanyahu ya yabawa Amurka

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda ke jagorantar yakin da ake yi da Iran, ya jinjinawa Trump bisa wannan mataki.

“Shawarar ka mai karfi na kai farmaki kan cibiyoyin nukiliyan Iran, da karfin ikon Amurka, zai canza tarihi, an sauke dukkan bama-bamai a babbar cibiyar, wato Fordow.
“Dukkan jiragen sun fita daga sararin samaniyar Iran. Su na kan hanyarsu ta komawa gida cikin lafiya.”

Wani jami’i na biyu ya ce kusan makamai masu linzami Tomahawk 30 aka harba daga jiragen ruwa na kasa da ruwa na Amurka.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce wannan mataki na Amurka “shiri ne na tada gaba ta yaki a dukan yankin.”

MDD ta soki harin Amurka a Iran

Mun ba ku labarin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta soki hare-haren da Amurka ta kai kan Iran, tana cewa suna barazana ga zaman lafiya a duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Tarihi bai manta ba: China ta tunawa duniya yadda Iran ta buga gwagwarmaya a baya

Sakataren MDD, Antonio Guterres ya ce yana cikin firgici saboda harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan wuraren nukiliya a Iran.

Guterres ya bayyana cewa "wannan lokaci mai hadari ne", yana kira da a kauce wa rikicin da zai janyo bala’i ga fararen hula da duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.