Isra'ila Ta Gargadi Jama'arta bayan Kasar Iran Ta Ragargaza Wani Asibiti

Isra'ila Ta Gargadi Jama'arta bayan Kasar Iran Ta Ragargaza Wani Asibiti

  • Makaman da Iran ta harba Isra'ila sun yi nasarar ragargaza muhimman wurare, daga ciki har da wani babban asibiti
  • Duk da hukumomin asibitin Soroka sun bayyana cewa an kwashe majinyata kafin harin, amma sun gargadi jama'a kan kusantarsa
  • Wani bidiyo a kafafen sada zumunta ya nuna jama'a suna kururuwa da neman dauki ta tagar asibitin bayan fadawar makaman

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Israel – Wani harin makami mai linzami daga Iran ya yi mummunan barna a wurare hudu a tsakiyar Isra’ila da kudu, daga ciki har da asibitin Soroka.

Daraktan asibitin, Shlomi Kodesh, ya ce harin da Iran ta kai da safiyar yau ya fada wani tsohon dakin tiyata da aka kwashe masu jinya da ke kwance a wurin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda, sun raunata shugaban ISWAP, Albarnawi

Iran ta sake harba makamai zuwa Isra'ila
Makaman Iran sun lalata wurare uku a Isra'ila Hoto: Getty
Source: Getty Images

Aljazeera ta ruwaito cewa Kodesh ya ce hukumomi na tantance irin barnar da aka yi, sannan ya bukaci jama'a su guji zuwa asibitin sai dai idan akwai bukatar agajin gaggawa.

Rahoton ya kara da cewa yayin da lamari ke rincabewa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu yana tantance matakin da zai dauka kan shiga yakin.

Isra'ila ta gargadi mutanenta

BBC ta ruwaito cewa wani jami’in sojan Isra’ila ya ce harin makami mai linzami da Iran ta harba a safiyar yau na daga cikin mafi muni da ta kai kasarsa.

Bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna hayaki ya tarnake asibitin Soroko yayin da mutane ke kururuwa suna neman dauki.

Isra'ila ta gargadi mutanenta
Isra'ila ce an kwashe marasa lafiya a asibitin da makam rIran suka fada Hoto: @Iran
Source: Getty Images

Wata mai magana da yawun asibitin ta ce:

“Asibitin ya fuskanci mummunar barna”.

An bukaci mutane su guji yankin saboda fargabar yaduwar wani sinadari mai haɗari daga makamain da kasar Iran ta harba.

Kara karanta wannan

Isra'ila: Iran ta umarci jama'a su daina amfani da whatsApp, ta fadi sharrin manhajar

Rahotannin sun tabbatar da cewa an kai hari sau uku a wasu sassa na kasar a daidai lokacin da aka farmaki babban asibitin Soroka.

Isra’ila ta kai hari a kasar Iran

Sojojin Isra'ila sun kai hari wani yanki da ke kusa da wurin binciken makamashin nukiliya a Arak, wanda ke cikin shirin nukiliyar Iran.

Tun da farko, rundunar tsaron Isra’ila ta bukaci mazauna garuruwan Arak da Khondab, wadanda ke kusa da filin, da su bar wurin domin tsira da rayukansu.

Hukumomi sun ce an kwashe mutanen da ke wurin kafin harin ya auku, don haka babu hadarin yaduwar guba.

Iran ta harba makamai masu hadari Isra'ila

A baya, mun kawo labarin cewa a ci gaba da musayar wuta, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake harba makamai masu linzami guda 30 a kan ƙasar Isra’ila.

An harba waɗannan makamai ne a dare biyu, yayin da faɗan dake tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsananta, yayin da Iran ta ce Isra'ila ce ba ta son zaman kafiya.

Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila (IDF), Birgediya Janar Effie Defrin, ya tabbatar da harin, inda ya ce an dakile yawancin makaman tun suna sama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng