Hajji: Matan Najeriya 3 Sun Yi Ɓarin Ciki a Saudiyya, An Samu Masu Cutar Hauka 13
- Hukumar NAHCON ta kula da akalla alhazai 15 masu tabin hankali da kuma mata uku da suka samu barin ciki a aikin Hajjin 2025 a Saudiyya
- Dr. Sani Garba ya bayyana kalubalen samun magungunan tabin kwakwalwa a Saudiyya inda ya ce dole suka rika kai su asibitin kasar
- A lokacin da alhazai ke Mina da Arafat, likitocin Najeriya sun kula da marasa lafiya 10,886 cikin akalla ofisoshi 20 da suka bude a tantuna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiyya - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta kula da marasa lafiya sama da 15 masu tabin hankali, da kuma wasu mata uku da suka yi ɓarin ciki.
Hakazalika, hukumar NAHCON ta ce ta kula da wasu marasa lafiya daban-daban a lokacin aikin Hajjin 2025 da aka kammala kwanan nan a Saudiyya.

Source: Facebook
Shugaban tawagar likitocin NAHCON, Dr. Sani Garba, ne ya bayyana haka yayin taron bayan kammala aikin Hajji da aka gudanar a birnin Makka ranar Talata, inji Daily Trust.
“Mun fuskanci kalubale matuka wajen kula da fiye alhazai 15 da ke fama da matsanancin ciwon hauka. Lamarin ya zamo mai matukar wahala a gare mu."
- Dr. Sani Garba.
Kalubalen samun magunguna a Saudiyya
Dr. Garba ya ce babban kalubalen da tawagarsu ta fuskanta shi ne samun damar mallakar magungunan da ake amfani da su ga masu tabin kwakwalwa a Saudiyya.
Ya bayyana cewa:
“Ba a yarda mun sayi irin wadannan magunguna ba. Abin da muke yi shi ne mu kai marasa lafiyar zuwa asibitin Saudiyya domin ayi masu allura, sannan mu dawo da su."
Ya ce sun ci karo da marasa lafiya da ke da tarihin cutar hauka a cikin iyalansu, amma ba su samu damar shigo da magungunansu ba, kuma an hana su shigo da su kasa mai tsarki.
Ɓarin ciki da karbar haihuwar alhazai mata
Dr. Garba ya ce an samu akalla mata hudu da suka yi fama da rashin lafiya saboda juna biyu da suke dauke da shi a lokacin aikin hajji, inda cikin uku daga cikinsu ya zube, yayin da daya ta haihu a Madina.
“Muna da rahoton mata hudu da ke dauke da juna biyu, uku sun samu barin ciki, daya kuma ta haihu a Madina. Jimillar wadanda suka rasu gaba daya a hajjin bana sun kai tara"
- Dr. Garba.

Source: Twitter
Yadda aka kula da marasa lafiya a Saudiyya
Punch ta rahoto shugaban tawagar ma'aikatan jinya na NAHCON ya bayyana cewa:
“A lokacin da alhazai ke a Mina da Arafat, tawagarmu ta kula da marasa lafiya 10,886 a cikin ofisoshinmu fiye da 20 da ke cikin tantuna.
“Maza 6,340 ne, mata kuma 4,546. Tun lokacin da aikin hajjin 2025 ya fara, an duba marasa lafiya 15,186; maza 8,460 da mata 6,726.”
Ya bayyana cewa mafi yawan marasa lafiyar sun kamu ne da matsanancin tsotsewar ruwan jiki saboda tsananin zafin rana da kuma cututtukan kwakwalwa.
- Dr. Garba.
Gobara ta tashi a masaukin alhazan Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, NAHCON ta tabbatar da cewa dukkanin mahajjatan Najeriya 484 da ke cikin otal ɗin da gobara ta tashi a Makkah sun tsira da rayukansu.
Gobarar ta tashi ne a otal ɗin Imaratus Sanan da ke kan titin Shari’ Mansur, inda kamfanonin jiragen yawo guda shida daga Najeriya suka saukar da mahajjatansu.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Pakistan, ya kai ziyara zuwa wurin da gobarar ta faru, inda ya bayar da umarnin a sauya masaukin mahajjatan.
Asali: Legit.ng


