Bayan Cacar Baki, Elon Musk Ya Yi Nadamar Zafafa Harshe ga Trump
- Attajirin duniya, Elon Musk, ya bayyana cewa yana nadamar wasu sakonnin da ya wallafa kan Shugaban Amurka, Donald Trump
- Musk ya ce maganganunsa sun yi tsauri fiye da kima, inda ya zargi Trump da shirya kasafin kuɗi mai illa ga tattalin arzikin Amurka
- Rigimar ta kara kamari ne bayan Trump ya ce bai da sha’awar gyara alaka da Musk, yana mai cewa ya ɓata masa rai sosai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shahararren attajiri kuma mai kamfanin Tesla, Elon Musk, ya fito fili ya bayyana nadamarsa game da wasu sakonni da ya wallafa kan Shugaban Amurka, Donald Trump.
Mista Elon Musk ya yi maganar ne bayan rikici ya yi kamari tsakaninsa da Donald Trump a kafafen sada zumunta.

Source: Twitter
Musk ya bayyana haka ne a ranar Laraba a shafinsa na X, inda ya ce wasu daga cikin sakonninsa sun wuce gona da iri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rigimar ta ƙara daukar hankali bayan da Trump ya bayyana a wata hira cewa ba zai sake gyara dangantaka da Musk ba, yana mai cewa attajirin ya ɓata masa rai sosai.
Musk ya goge wasu sakonnin da ya wallafa
BBC ta wallafa cewa bayan ce-ce-ku-cen da lamarin ya haddasa, Musk ya goge yawancin sakonninsa a karshen makon jiya.
An ruwaito cewa cikin sakonnin da ya goge har da wanda ya bukaci Trump ya sauka daga mulki, da wani da ya yi ikirarin cewa shi ne ya taimaka wa Trump wajen lashe zaɓe.
Musk ya kasance wanda ya tallafa wa takarar Trump a 2024, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin masu kusanci da shugaban.
Sai dai rigimar tasu ta barke ne bayan Musk ya yi murabus daga wani sabon ofishi da ake kira DOGE da ya rike na tsawon kwanaki 129 kacal.
Me ya hada Elon Musk da Donald Trump?
Tun da farko, Musk ya nuna damuwa kan sabon kasafin kuɗi da Majalisar Wakilai ta amince da shi, da ke kunshe da gagarumar kashe kuɗi kan tsaro da rage haraji ga wasu masu arziki.
Ya bukaci ‘yan Amurka da su tuntubi wakilansu a Washington domin hana dokar samun amincewa daga Majalisar Dattawa.
Elon Musk ya yi magana ne yana mai cewa kasafin za ta jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki a nan kusa kadan.

Source: Getty Images
Zargin da Elon Musk ya yi wa Trump
Musk ya yi ikirarin cewa akwai wasu bayanai daga cikin takardun gwamnati da ba a fitar da su ba da ke da alaƙa da Trump da marigayi mai laifin lalata da yara, Jeffrey Epstein.
Duk da Musk bai gabatar da hujja ba, fadar White House ta mayar da martani da cewa zargin ba shi da tushe.
An hana 'yan Amurka shiga Chadi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Mahamat Idriss Deby ya saka dokar dakatar da Amurkawa shiga kasar Chadi.
Mahamat Deby ya dauki matakin ne bayan shugaban, Amurka Donald Trump ya hana wasu kasashe shiga kasarsa, ciki har da Chadi.
A martanin da ya yi wa Trump, Deby ya ce Chadi ba ta da makudan kudi amma kuma tana da martaba da kima da zai hana ta yarda da kaskanci.
Asali: Legit.ng

