Hajjin Bana: Mahajjaciyar Najeriya Ta Rasu a Asibitin Makkah

Hajjin Bana: Mahajjaciyar Najeriya Ta Rasu a Asibitin Makkah

  • Wata mata mai shekaru 75 daga Jihar Edo, Adizatu Dazumi, ta rasu a Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana na 2025
  • An ce Dazumi ta kamu da rashin lafiya bayan kammala dawafi a Ka’aba, sannan aka garzaya da ita asibitin Sarki Fahad da ke birnin Makkah
  • Hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Edo ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce an birne ta bisa tsarin Musulunci a kasar Saudiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata mahajjaciya daga Jihar Edo mai suna Hajiya Adizatu Dazumi ta rasu yayin gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Rahotanni sun nuna cewa matar tana da shekaru 75 a duniya, kuma asalinta daga Jattu Uzairue da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma ta ke.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da limamin da zai yi wa miliyoyin Musulmai hudubar Arafa

Hadiza
'Yar Najeriya ta rasu a aikin Hajjin 2025. Hoto: Interlegion
Source: UGC

Rahoton Punch ya nuna cewa matar ta kamu da rashin lafiya ne bayan kammala dawafi a Ka’aba, sannan aka garzaya da ita zuwa asibitin King Fahad da ke Makkah a ranar Lahadi.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na Jihar Edo, Musah Uduimoh ya tabbatar da rasuwar a ranar Talata, inda ya ce an sanar da iyalanta kuma an birne ta a Makkah.

Yadda mahajjaciyar Najeriya ta rasu

Uduimoh ya bayyana cewa Adizatu Dazumi ta kamu da ciwo ne bayan ta kammala dawafi, wato zagaye dakin Ka’aba, wanda yana daga cikin ibadojin Hajji.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce:

“An kai ta asibiti a ranar Lahadi bayan ta fara jin rashin lafiya. Sai dai, da safiyar Litinin, sai Allah ya karɓi rayuwarta a asibitin Sarkki Fahad da ke Makkah.”

Ya ƙara da cewa an yi jana’izarta bisa tsarin Musulunci a ranar da ta rasu, sannan an sanar da danginta da ke Jattu Uzairue a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

Ita ce ta farko da ta rasu daga Najeriya

Wannan rasuwar ita ce irinta ta farko da aka samu daga cikin mahajjatan Najeriya a bana, kamar yadda rahotanni suka nuna.

A cewar hukumar, mahajjatan Jihar Edo da suka halarci aikin Hajjin bana sun kai 206, kuma an tashi da su daga Najeriya ranar 15 ga Mayu, 2025.

Rasuwar Adizatu ta jefa wasu cikin damuwa, amma hukumar ta ce tana kokarin tabbatar da lafiyar sauran mahajjata, tare da ƙara kulawa da yanayin kiwon lafiya a sansanonin su.

Tanadin addini ga mahajjacin da ya mutu

Malamin addini, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzri ya yi wa Legit karin haske kan mutuwar mahajjaci.

Malamin ya ce addini ya bayyana cewa idan mutum ya niyyar yin Hajji kuma ya rasu kafin shiga harami, Allah zai ba shi lada bisa niyyarsa kuma za a iya yi masa Hajji daga baya.

Sheikh Usman ya ce:

"Amma idan ya riga ya shiga harami kuma ya rasu, za a ba shi lada tamkar ya kammala aikin Hajji. Kuma ba sai an sake yi masa Hajji ba."

Kara karanta wannan

'Akwai hadari:' Amnesty Int'l ta soki shirin mika Hamdiyya ga 'Yan sanda

An hana Sheikh Gumi zuwa Hajjin 2025

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta hana malamin Musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi aikin Hajji.

Sheikh Gumi da kansa ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya ce yana gida Najeriya domin cigaba da noma.

Malamin ya yi zargin cewa abubuwan da yake fada a kan siyasar Gabas ta Tsakiya ne da ba su yi wa Saudiyya dadi dalilin hana shi zuwa Hajji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng