Sallar Layya: Kasar Saudiyya Ta Fitar da Sanarwar Duba Jinjirin Wata
- Kotun Kolin Saudiyya ta nemi al’ummar Musulmi da su fita duba jinjirin watan Dhul Hijjah a daren Talata 27 ga Mayu, 2025
- Bayyanar jinjirin watan ne zai nuna ko an shiga watan Dhul Hijjah, wanda ke dauke da ayyukan aikin Hajji da bukukuwan Sallah
- A Najeriya, ana sa ran mai alfarma Sarkin Musulmi zai fitar da sanarwa ga al’ummar Musulmi domin fara neman jinjirin watan a fadin kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta Saudiyya ta fitar da wata sanarwa tana kiran al’ummar Musulmi da mazauna kasar da su fara neman jinjirin watan Dhul Hijjah na 1446.
Saudiyya ta bukaci fara duba watan ne a yammacin Talata, 27 ga Mayu 2025 wanda ya dace da 29 ga watan Dhul Qa’ada na shekarar Hijira.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin duba watan ne a cikin wani sako da shafin kasar Saudiyya na Inside Haramain ya wallafa a X.
Wannan kiran ya zo ne domin tantance ko an ga jinjirin watan, wanda hakan ke nuna shigowar Dhul Hijjah, wata mai muhimmanci a Musulunci da ke dauke da aikin Hajji da bikin Sallah.
Kotun koli ta bayyana cewa duk wanda ya ga jinjirin da idonsa ko ta hanyar na'urar hangen nesa ya sanar da kotu mafi kusa da shi domin tabbatar da ganin watan.
An fara shirin Sallar layya a Saudiyya
Watan Dhul Hijjah na dauke da manyan ibadu a Musulunci, ciki har da aikin Hajji da kuma bikin babbar Sallah da Musulmi ke yi a ranar 10 ga watan bayan ibada a filin Arafa a ranar 9g ga wata.
A cewar Kotun Kolin, ganin jinjirin watan zai tabbatar da ranar farko ta Dhul Hijjah, wanda hakan zai bawa mahajjata damar shirye-shiryen karshe kafin fitowa zuwa Arafat.
Ana sa ran sanarwar Sarkin Musulmi a Najeriya
A Najeriya, ana kan sa ido kan sanarwar da za ta fito daga ofishin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda ke da alhakin bayyana ganin jinjirin wata.
Yayin da yau ke matsayin 28 ga watan Dhul Qa’ada, ana sa ran Sarkin Musulmi zai fitar da sanarwa a daren yau ko gobe.

Source: Facebook
Kamar yadda aka saba, sanarwar za ta kunshi umartar Musulmi su fara neman jinjirin watan a yankunansu da ke cikin dukkan birane da kauyukan kasar.
Sanarwar Sarkin Musulmi na da matukar tasiri wajen tsayar da ranakun ibada da bukukuwa a Najeriya, musamman a tsakanin Musulmi da ke bin kalandar Hijira.
An hana Sheikh Gumi zuwa Saudiyya aikin Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ba zai yi aikin Hajji bana ba.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa ba zai samu zuwa aikin Hajji ba ne saboda rashin amincewar kasar Saudiyya.
Malamin ya yi zargin cewa an hana shi shiga kasar ne saboda abubuwan da yake fada game da siyasar Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

