Da Gaske An Hana 'Yan Najeriya da Wasu Kasashe 13 Shiga Saudiyya? Gaskiya Ta Fito
- Hukumomin Saudiyya sun musanta rahoton da ke cewa an hana wasu kasashe 13 biza, ciki har da Najeriya, Jordan, Sudan da Iraq
- An ce dokar hana bizar za ta fara aiki daga 13 ga Afrilu, kuma duk wanda ya karya ta zai fuskanci haramcin shiga Saudiyya na shekaru
- Cibiyar yawon bude ido ta Saudiyya ta karyata rahoton, amma ta ce an takaita shiga Makkah ga masu yawon shakatawa lokacin Hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiyya - Hukumomin Saudiyya sun karyata wani rahoto da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke cewa kasar ta kawo sababbin takunkuman biza da haramcin shiga cikinta.
Rahoton da aka yada ya bayyana cewa Najeriya, Jordan, Sudan, Iraq, Indonesia, Habasha da Bangladesh na daga cikin jerin kasashen da aka dakatarwar neman biza yashafa.

Asali: Twitter
Saudiyya ta hana kasashe 13 shiga kasarta?
Rahoton jaridar Cable ya nuna cewa Saudiyya, ta hana kasashe 13 neman sababbin biza, ciki har da bizarn kasuwanci, ziyara (na lokaci guda/ko na lokaci-lokaci), yawon shakatawa da kuma ziyarar dangi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon umarnin ya kuma hada da sunayen kasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisia, Yemen da Algeria a cikin jerin kasashen da aka ce takunkumin zai shafa.
An bayyana cewa wadannan takunkuman za su fara aiki daga ranar 13 ga Afrilu, 2025 kamar yadda daftarin sabon umarnin ya nuna.
Haka nan an ce mutanen da ke da biza daga cikin wadannan kasashen ba za a bari su shiga Saudiyya daga ranar da abin zai fara aiki ba, koda kuwa suna da sahihiyar takardar shiga.
“Rashin bin wannan umarni na iya sa wa a hana mutum shiga Saudiyya na shekaru 5,” in ji sanarwar.
Saudiyya ta karyata wannan jita-jita
Sai dai, a lokacin da jaridar ta tuntube ta, cibiyar yawon shakatawa ta Saudiyya ta nesanta kanta daga wannan rahoto, tana mai cewa ba sanarwar hukuma ba ce.
Cibiyar ta shaida wa jaridar cewa takardar da hukumomin Saudiyya suka fitar na baya-bayan nan ta shafi ka’idojin aikin Hajji ne kawai.
Cibiyar, ta sanar da cewa:
“Babu izinin gudanar da aikin Hajji ko shiga birnin Makkah ga masu bizar yawon bude ido daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 11 ga Yunin 2025, (01 Thul Quda zuwa 14 Thul Hijjah 1446 AH)
Bizar yawon bude ido ba ta aikin Hajji

Asali: Twitter
Bizar aikin Hajji ana bayar da ita ne kawai domin aikin Hajji, kuma tana aiki ne kawai a lokacin wannan ibada ta Musulmi.
Musulmai da ke son ziyartar Saudiyya domin aikin Hajji dole ne su nemi bizar Hajji ta musamman, ba ta yawon bude ido ba.
Wannan tabbatarwa da aka samu daga mahukuntan Saudiyya, ya kawo karshen wannan rudani da aka samu game da shigar 'yan Najeriya kasar mai tsarki.
Saudiyya ta hana Umarah sau 2 a Ramadan
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da cewa ba za a bar alhazai su yi Umrah fiye da sau ɗaya a watan Ramadana ba.
An bullo da wannan tsari ne domin rage cunkoson jama’a da ake fuskanta a wannan wata mai alfarma, wanda ke jawo yawan masu Umrah fiye da kowanne lokaci.
Hukumar ta bukaci jama’a da su bin doka da oda, domin gujewa matsaloli tare da bai wa kowa damar sauke Umrah cikin sauki da tsari a Ramadana.
Asali: Legit.ng