An kara ka'idojin zuwa hajin bana (Karanta)

An kara ka'idojin zuwa hajin bana (Karanta)

- Sabbin tare-tsaren da hukumar alhazan Najeriya ta fito dasu na samun karbuwa daga masana alamuran aikin hajin a kasar

- Cikin sabbin tsare-tsaren babu wanda za'a bari ya tafi aikin haji sai ya samu mai tsaya masa ya kuma sa hannu cikin takardar neaman zuwa hajin

An kara ka'idojin zuwa hajin bana (Karanta)
An kara ka'idojin zuwa hajin bana (Karanta)

Ana bukatar duk mai niya ya samu mai-unguwa ko wani babban jami'in gwamnati dake kan albashi na 14 ko fiye ya tsaya masa.

Baicn wannan hukumar tayi sabon tsarin bada kudin guzuri ga alhazan. A sabon tsarin hukumar alhazan ke da alhakin baiwa alhazan kudaden guzurinsu ta hanyar bankuna maimakon yadda ake yi da inda jihohi ke bayarwa.

KU KARANTA: An kafa kwamiti don sulhunta Elrufa'i da Shehun Sani

Matakin samun wanda zai tsayawa maniyyaci zai taimaka wajen rage yawan masu batawa kasar Najeriya suna, inji kakakin hukumar Alhaji Uba Malam.

Alhaji Uba yace duk wanda zai tsayawa mutum dole ya tabbatar mutumin kwarai ne, nagari wanda ba zai aikata aikin asha ba ya batawa kasa suna. Shi ya sa hukumar ta bada shawara duk wanda zai tafi aikin haji a tabbatar mutum ne nagari.

Hukumomin jin dadin alhazai na jihohin Najeriya sun ce sun dauki matakin ganin an ci nasarar gudanar da sabbin tsare-tsaren kamar yadda shugaban hukumar alhazan jihar Neja Alhaji Adamu Cabi ya bayyana. Yace sun riga sun raba takardun neman tafiya kuma da zara sun ga sa hannu hakimi ko jami'in gwamnati wanda yake kan albashi akalla mataki na 14 sai su amince.

Masanin harkokin aikin haji kuma sakataren kungiyar IZALA reshen jihar Neja Alhaji Aminu Kagara yace sun yi maraba da sabbin tsare-tsaren. Yace sabbin matakan zasu yi maganin matsalolin da aka fuskanta can baya.

Ko baicin kama alhazan jihar Kwara da tarin kwaya a shekarar bara a can Saudiya bayanai sun nuna cewa kimanin alhazan Najeriya 396 ne suka makale a kasar Saudiyan bayan kamala aikin haji.

KU CI GABA DA BIYO MU A FACEBOOK DA KUMA TUWITA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng