'Ana Neman Ƴan Uwansu': Ƴan Najeriya 60 Sun Mutu a Birtaniya, Sun bar Tarin Dukiya

'Ana Neman Ƴan Uwansu': Ƴan Najeriya 60 Sun Mutu a Birtaniya, Sun bar Tarin Dukiya

  • Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jerin kadarorin marayu da har yanzu ba a karɓa ba, ciki har da kadarori 60 da ke da alaƙa da 'yan Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa yawancin mamatan maza ne, kuma sun fito ne daga Legas, sai dai akwai kaɗan daga wasu jihohin dabam
  • Birtaniya ta shawarci ƴan uwan waɗanda suka mutu da su gabatar da hujjoji don karɓar kadarorin da mutanen suka mutu suka bari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Birtaniya - Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jerin kadarorin da masu su suka mutu, amma har yanzu babu wani magajinsu da ya je ya karɓe su.

A cikin sunayen kadarorin da ofishin babban lauyar Birtaniya ya fitar, an ce kimanin 60 na ƴan Najeriya ne, da suka zauna a ƙasar.

Gwamnatin Birtaniya ta magantu da 'yan Najeriya 60 suka mutu suka bar dukiyar da babu masu gado
Ana fargabar 'yan Najeriya 60 sun mutu sun bar dukiyarsu a Birtaniya ba tare da magada ba. Hoto: Kapook2981
Asali: Getty Images

'Yan Najeriya sun mutu sun bar dukiya a Birtaniya

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Daga cikin wadannan mutane 60, an ce maza ne suka fi yawa a cikinsu, kuma jihar Legas ce jihar da suka fi fitowa daga cikinta, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaɗan daga cikin mutanen sun kasance ‘yan asalin jihohi irin su Rivers da Ondo, yayin da wasu ‘yan kalilan aka haifa a Birtaniya.

Yawancinsu ba su da aure, kuma babu wata alama da ke nuna 'yan uwansu da za su gaji arzikin da suka bari.

Sai dai wani Charles Ayodele Aliu, da aka haifa a Nuwamba 1935, da ake tunanin yana da ɗan uwa a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan wadanda suka rasu, an haife su ne a tsakanin shekarun 1930 zuwa 1940, inda mafi tsufa a cikinsu, aka haife shi a 1919.

A yayin da mai ƙaramin shekaru a cikinsu aka haife shi a 1994, ana ganin hakan ya nuna gagarumar hijirar ƴan Najeriya zuwa Birtaniya a tsakiyar ƙarni na 20.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Wasu daga cikin kadarorin da ba a karba ba

Rahoton ya nuna cewa mafi yawan mutanen sun mutu ne a Landan da kewayenta, yayin da wasu suka mutu a Birmingham, Leeds, Sheffield, da Derby.

An kuma lura cewa wasu daga cikin ‘yan Najeriyan sun canja sunayensu kwata-kwata ko sun sauya tsarin sunayen, ya sa ba a iya gano magadansu ba.

An ce manya da kananan hukumomin Birtaniya ne suka fitar da bayanin kadarorin, ciki har da Barclays, Santander, HSBC da TSB ne suka ruwaito su.

Haka kuma, an ce akwai wasu asibitoci ko hukumomin lafiya da ruwaito wasu daga cikin kadarorin, da har yanzu babu wanda ya gaje su.

Birtaniya na neman ƴan uwan waɗanda suka mutu

Ofishin harkokin cikin gida na Birtaniya ya shawarci duk wanda ke da'awar yana da gadon dukiyar ɗan uwansa da ya rasu, da ya gabatar da hujja don karbar kadararsa.

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

The Cable ta ce wadannan hujjojin sun haɗa da bayanan haihuwa, aure, da takardar rasuwar duk mutanen da ke da alaƙa da wanda ya mutu.

Ana iya duba cikakken jerin kadarorin da ba a karɓa baa shafin gwamnatin Birtaniya.

A kowace shekara, dubban mutane suna mutuwa a Birtaniya ba tare da barin wasiyya ba ko bayyana danginsu da su iya gadar dukiyarsu ba.

Cikin waɗannan akwai ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka, wadanda a ƙarshe ake barin ikon mallakar kadarorin da suka bari a hannun Sarauniyar Ingila.

Rashin wasiyya na jawo asarar dukiya

Rahoto ya nuna cewa rashin barin wasiyayya na sanya kadarorin da aka mallaka a Birtaniya su koma hannun gwamnati
Yadda rashin wasiyya ke sa 'yan uwa su rasa kadarorin 'yan uwansu da suka mutu suka bari a Birtaniya. Hoto: hija
Asali: Getty Images

Ga yawancin ‘yan gudun hijira, Birtaniya ta zama ƙasar da suke son zama a cikinta, inda suke tara arziki, su sayi kadarori, kuma suka kafa rayuwa mai kyau.

Sai dai rashin barin wasiyya yana sa kadarorinsu su koma hannun gwamnati a matsayin "bona vacantia" (dukiyar da ba ta da magada) idan sun mutu.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

A lokuta da dama, iyalai da ƴan uwa a Afirka ba su da masaniya game da wannan dukiyar da ɗan uwansu ya bari, lamarin da ke sa ta salwanta har abada.

Akwai misali Adenike Adebiyi, wacce ta rasu a Hackney, London, a 2004, da kuma Solomon Adekanmibi, wanda ya mutu a Colchester, Essex, a 2021, duka sun gamu da irin wannan matsala.

Ana zargin Seyi Tinubu ya saye gida a Landan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani kamfani mallakin Seyi Tinubu ya kashe $11m wajen sayen katafaren gida da ke ƙarƙashin binciken gwamnatin tarayya a Birtaniya.

Bincike ya bayyana cewa ɗan shugaban kasar Najeriya ya sayi gidan da ke Landan, wanda ake zargin an mallake shi ne da kuɗin haram, kuma ana zargin da hannun Tinubu a ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng