Kunne ya girmi kaka: Hausawan farko da suka fara zuwa Birtaniya (HOTO)
Wani ma’abocin jaridar Rariya Imam Ghazali Umar ya rubuta sharhi kan hausawan da suka fara taka kafarsu a kasar Birtaniya tun a zamanin baya.
A cewar majiyar Legit.ng, Hausawan da suka fara isa kasar Birtaniya sune Abbega da Dorugu, inda shi Dorugu bahaushene cikakke da aka haifa a shekarun 1839 a kasar Damagram, Zinder a yanzu.
KU KARANTA: Yadda ɗan Boko Haram ya lahanta wani yaro a daren da suka sace yan matan Chibok
Sai dai an bayyana dayan mutumin mai suna Abbega a matsayin mutumin Margi ne, amma saboda cudanyarsu da hausawa yaji hausa sosai.
Dalilin su zuwa kasar Ingila kuwa shine, an siyar dasu a matsayin bayi ne, haka dai har suka fada hannun shahararen masanin nan mai yawon bude ido Henrich Berth dan kasar Jamus, inda ya tafi dasu kasar Ingila a shekarar 1855.
A zamansu na kasar Ingila suka yi kicibus da wani marubuci, mai sha’awar yaren Hausa, JF Schon, inda a hannunsa ne suka sauya addini zuwa Kiristanci, sa’annan suka taimaka masa wajen rubuce rubucensa da yaren Hausa.
Tarihi ya nuna cewar bayan kwashe shekaru da dama, Abbega ya dawo gida Najeriya, inda har ya samu mukanin sarauta a garin Lokoja a shekarar 1896, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Shi ma Dorugu ya dawo Najeriya, har ma ya koyar a wata makarantar Sojoji dake garin Lokoja, daga bisani kuma ya koma kwalejin Dan Hausa dake jihar Kano.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Yadda aka kashe Hausawa a Ife, Kalli:
Asali: Legit.ng