Bayan Gwabza Fada, Sojoji Sun Kwace Iko a Fadar Shugaban Kasar Sudan
- Dakarun sojin Sudan sun sanar da cewa sun karbe cikakken iko da fadar shugaban kasa a birnin Khartoum
- Sojojin Sudan sun kwato wasu wurare daga hannun dakarun RSF, yayin da RSF ke karfafa ikonta a Yammacin kasar
- Fadan da ke gudana ya haddasa bala'i mafi girma a duniya, inda yunwa da cututtuka suka yawaita a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sudan - Dakarun sojin Sudan sun sanar da cewa sun kwato fadar shugaban kasa da ke tsakiyar birnin Khartoum, bayan shafe shekaru biyu suna fafatawa da rundunar 'yan tawayen RSF.
Ana ganin cewa nasarar ta zama daya daga cikin nasarorin da suka fi girma tun bayan barkewar rikici a kasar.

Asali: Getty Images
Rahoton Reuters ya nuna cewa baya ga kwace fadar shugaban kasa, sojojin sun bayyana cewa sun karbe iko da wasu ma’aikatun gwamnati da gine-gine masu muhimmanci a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BBC ta wallafa cewa dakarun RSF sun ja da baya da nisan kimanin mita 400 daga wuraren da sojojin suka kwace.
Yadda rikicin kasae Sudan ya kara tsananta
Tun bayan barkewar fada a Afrilun 2023, RSF ta kwace Khartoum, ciki har da fadar shugaban kasa, sakamakon takaddamar da ta taso dangane da shigar da dakarunta cikin sojojin Sudan.
Yayin da sojojin ke samun galaba a Khartoum, RSF kuwa na ci gaba da karfafa matsayinta a Yammacin kasar, inda take kokarin kafa gwamnatin da ba ta da cikakken karbuwa a idon duniya.
Duk da cewa ana hasashen gwamnatinsu ba za ta samu karbuwa a duniya ba, hakan na nuni da yiwuwar rarrabuwar Sudan zuwa bangarori biyu.
Al’umma sun nuna farin ciki da nasarar sojoji
Wasu daga cikin mazauna Khartoum sun bayyana kwato fadar shugaban kasa a matsayin gagarumar nasara ga dakarun kasar.

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno
Wani mazaunin Khartoum mai suna Mohamed Ibrahim ya ce:
“Kwato fadar shugaban kasa ne labari mafi dadi da na ji tun farkon wannan yaki. Wannan na nufin sojoji za su kwato sauran birnin Khartoum.”
Sai dai har yanzu ana jin harbe-harbe a wasu yankunan birnin, inda ake sa ran fadan zai kara tsananta yayin da sojojin ke kokarin fatattakar RSF daga kudancin Khartoum.
Matsalar jin kai na kara tabarbarewa a Sudan
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin Sudan a matsayin bala’i mafi muni a duniya, inda yunwa da cututtuka suka addabi mutane sama da miliyan 50.
Ann zargi bangarorin da aikata laifuffukan yaki, yayin da RSF ke fuskantar zargin aikata kisan kare dangi, amma sun musunata zargin.

Asali: Getty Images
Sojojin Sudan sun sha alwashin ci gaba da yaki har sai sun kwato duka yankunan kasar. A cikin wata sanarwa, sojojin sun ce:
“Za mu ci gaba da tunkarar abokan gaba har sai mun tsarkake kowace kusurwa ta kasar mu daga wadannan ‘yan tawaye.”
Rahotanni sun nuna cewa rikicin Sudan ya samo asali ne bayan hambarar da tsohon shugaban kasa Omar al-Bashir a 2019.
Duk da cewa sojojin Sudan da RSF sun hada kai wajen kifar da mulkinsa, sai dai daga baya suka fara sabani, wanda hakan ya jawo wannan yaki mai tsanani.
An ceto wasu 'yan Najeriya a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da ceto wasu jarirai da rikicin Gaza a kasar Falastinu ya ritsa da su.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tauggar ya bayyana matakin da Najeriya ta dauka domin kubutar da su daga luguden wuta a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng