Abubuwan da Suka Jefa Kasar Nijar Wahalar Fetur har Ta Nemi Agajin Najeriya

Abubuwan da Suka Jefa Kasar Nijar Wahalar Fetur har Ta Nemi Agajin Najeriya

  • Kasar Nijar na fama da wani matsanancin karancin fetur, lamarin da ya haddasa dogayen layuka a gidajen mai
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa safarar man fetur daga Najeriya zuwa Nijar na karuwa sakamakon matsalar
  • Hukumar mai ta Nijar ta ce kamfanin SORAZ ba zai iya samar da isasshen mai ba don biyan bukatun 'yan kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun nuna cewa kasar Nijar na fuskantar matsanancin karancin man fetur, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin mai da kuma dogayen layuka a gidajen mai.

Rahotani su nuna cewa matsalar ta kara ta’azzara ne bayan da Nijar ta fice daga kungiyar ECOWAS.

Kasar Nijar
Abubuwan da suka jefa Nijar matsalar man fetur. Hoto: Habu Abdullahi
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa babban daraktan kasuwanci na kamfanin man Nijar, Maazou Aboubacar, ya bayyana dalilin shiga matsalar.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Dalilin da ya sa za a gudanar da azumin Ramadan sau 2 a 2030

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin shiga matsalar fetur a kasar Nijar

Maazou Aboubacar ya ce daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa wannan matsala shi ne rashin samun man fetur daga kasuwar bayan fage, wanda ke fitowa daga Najeriya.

A cewarsa, a halin yanzu, kamfanin SORAZ na samar da tankar mai 25 ne kacal a kullum, alhalin bukatar kasar Nijar ta nunka hakan.

Rahotanni sun kuma nuna cewa gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta rage farashin mai tun bayan karbar mulki a shekarar 2023, wanda hakan ya kara bukatar man fetur a cikin kasar.

Nijar ta kori jami’an kamfanin man China

A wani mataki na karfafa ikon mulkinsa kan arzikin kasa, gwamnatin soja ta Nijar ta umarci wasu jami’an kasar China da ke aiki a fannin mai su fice daga kasar.

Wata majiya ta shaida Punch cewa gwamnatin Nijar ta bukaci manyan jami’ai uku daga kamfanin China na CNPC, WAPCo, da SORAZ su fice daga kasar nan take.

Kara karanta wannan

Lamura na neman tsayawa cak a Nijar, Tchiani ya bukaci taimakon Tinubu

Wasu mazauna yankunan da ke iyaka da Najeriya a jihohin Sokoto, Katsina, Jigawa, Yobe da Borno sun ce matsalar karancin man fetur ta haddasa dogayen layuka a gidajen mai da ke Nijar.

Biyo bayan haka, wasu mazauna kasar na sayen mai a kasuwar bayan fage maimakon su tsaya a layuka.

Safarar fetur ta karu a iyakokin Najeriya da Nijar

Shugaban wata al’umma da ke Maigatari, jihar Jigawa, ya tabbatar da cewa gidajen mai a Nijar sun rufe tsawon kusan watanni biyu sakamakon rashin man fetur.

Ya ce wani manajan gidan mai a Dingas, Nijar, ya bayyana masa cewa ya shafe fiye da kwanaki 40 babai samu mai ba, lamarin da ya ce bai taba faruwa ba a tarihi.

Shugaban ya ce:

“Akwai hanyoyin da jama’a ke amfani da su wajen safarar man fetur zuwa Nijar. Muna da dangantakar zumunta da juna, kuma ba za mu bar junanmu cikin wahala ba,”

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

'Yan gudun hijira sun shiga safarar man fetur

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa garuruwa da kauyuka da ke iyaka da Najeriya a Yobe da Borno kamar Geidam, Machina, da Kanamma sun shiga safarar man fetur zuwa Nijar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa farashin mai a Nijar ya yi tashin gwauron zabi:

“A garuruwa irin su Gidigir, Dumar, Malawa, Ngamdu da Fune, ana sayar da lita daya na mai tsakanin CFA1,200 zuwa CFA1,400, wanda ya kai kusan N2,500 zuwa N2,900.
"Amma idan aka shiga cikin Nijar sosai, farashin yana kara hawa.”
Gidan mai
Yadda ake layin a wani gidan mai. Hoto: Kola Sulaimon.
Asali: Getty Images

Nijar ta nemi tallafin mai daga Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin sojin Nijar ta nemi taimakon fetur daga Najeriya bayan shiga matsalar mai a 'yan kwanakin bayan nan.

Legit ta rahoto cewa gwamnatin Najeriya ta nuna dattaku wajen tura tankokin man fetur kasar Nijar duk da tangardar diflomasiya a tsakanin kasashen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng