Bayan Taimakon Nijar, Najeriya Ta Fadi Haɗarin da Ke Tunkaro Ta daga Makwabtanta

Bayan Taimakon Nijar, Najeriya Ta Fadi Haɗarin da Ke Tunkaro Ta daga Makwabtanta

  • Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya ce Najeriya na cikin hadari idan Nijar, Mali da Burkina Faso ba su koma mulkin dimokuradiyya ba
  • Janar Musa ya ce gazawar shugabanci da talauci a wadannan kasashe na barazana kai tsaye ga Najeriya, kuma yana haifar da matsaloli
  • Gwamnatin tarayya na kokarin karfafa tsaron iyakoki don kaucewa barazanar tsaro daga makwabtan kasashen da ke fama da rikice-rikice
  • Hafsun sojan ya ce duk da cewa rahoton duniya ya saka Najeriya a matsayi na shida a ta'addanci, tsaro ya inganta sosai a cikin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, ya yi magana kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Janar Musa ya ce Najeriya na fuskantar babban hadari idan kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ba su dawo mulkin dimokuradiyya ba.

Kara karanta wannan

Lamura na neman tsayawa cak a Nijar, Tchiani ya bukaci taimakon Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta jero matsalolin da ke tunkararta daga makwabta
Najeriya ta bukaci kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso su dawo mulkin dimukradiyya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Nijar & Mali: Haɗarin da ke tunkaro Najeriya

Hafsan tsaron ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a 15 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Musa ya ce gazawar shugabanci a wadannan kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso na shafar Najeriya kai tsaye.

Janar Musa ya ce:

“Na fada a baya, muna da matsalolin talauci a yammacin Afirka, da kuma matsalolin shugabanci a Nijar, Mali da Burkina Faso.
“Suna fuskantar matsaloli da yawa, saboda yankunan sun kasance manya, akwai talauci mai yawa, da sauyin yanayi, da kuma rashin kyawun shugabanci.”
“Kuma wadannan matsalolin suna kokarin shigowa cikin Najeriya, duk wani yunkuri da muke yi, zai ci gaba da fuskantar kalubale.”
“Gaskiyar magana, musamman a wadannan kasashe ukun, yana da muhimmanci su samu shugabanci nagari da zai iya inganta al’umma."
An bukaci Nijar da sauran ƙasashe makwabtanta su dawo mulkin dimukradiyya
Najeriya ta fadi haɗarin da ke tunkaro ta daga ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso. Hoto: Bayo Onanuga, Muhammad Badamasi.
Asali: Facebook

An bukaci Nijar, Mali su watsar da mulkin soja

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Shugaban tsaron ya ce shiyasa suke ta burin samar da shugabanci nagari a wadannan kasashe, cewar TheCable.

Ya kara da cewa:

“Shi ya sa muke cewa, idan ba su samu shugabanci nagari ba, Najeriya na da yawan abin da za ta rasa, dole ne su koma mulkin dimokuradiyya.”

Musa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokari wajen karfafa tsaron iyakoki da wadannan kasashe don kaucewa barazanar tsaro.

Da yake bayani kan sabon rahoton “global terrorism index”, Musa ya ce kodayake Najeriya na matsayi na shida, tsaro ya samu gagarumar ci gaba.

“Shi ya sa gwamnati ke daukar mataki wajen inganta tsaron iyaka domin kare kasa, saboda iyaka ce hanya mafi rauni.
“Ba zan yi magana a madadin yammacin Afirka ba, zan yi a madadin Najeriya. A shekarar 2024, mun fi samun karancin hare-hare a cikin kasa.”
“Abubuwa na ingantuwa, duk da cewa akwai ‘yan matsaloli a wurare daban-daban, sojoji na kokari matuka wajen ganin sun kare kasa.”

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

- Cewar Janar Christopher Musa

Najeriya ta taimakawa Nijar

Mun ba ku labarin cewa rashin man fetur ya hana harkokin kasuwanci da zirga-zirga a Nijar tsawon makonni biyu.

Rahotanni sun ce gwamnatin mulkin sojan Nijar ta tura wakilai zuwa birnin Abuja domin rokon Najeriya ta tura mata mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel