Lamura na Neman Tsayawa Cak a Nijar, Tchiani Ya Bukaci Taimakon Tinubu

Lamura na Neman Tsayawa Cak a Nijar, Tchiani Ya Bukaci Taimakon Tinubu

  • TinuRahotanni na nuni da cewa rashin man fetur ya hana harkokin kasuwanci da zirga-zirga a Nijar tsawon makonni biyu.
  • An ruwaito cewa gwamnatin mulkin sojan Nijar ta tura wakilai zuwa birnin Abuja domin rokon Najeriya ta tura mata mai
  • Biyo bayan lamarin, Najeriya ta amince da bayar da taimako ta hanyar aikawa da motoci 300 cike da mai zuwa jamhuriyyar Nijar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsawon makonni biyu, Jamhuriyar Nijar ta fuskanci matsananciyar matsalar fetur, wanda ya jefa kasuwanci da zirga-zirga cikin mawuyacin hali.

Lamarin ya kai ga gwamnatin mulkin soja ta Nijar, wadda ta sha nuna ƙyamar alaka da ECOWAS, ta nemi agajin Najeriya domin samun mai.

Tchianii
Nijar ta nemi tallafin Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Muhammad Badamasi
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa duk da takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu, Najeriya ta amince da tallafawa Nijar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karancin man fetur a Nijar

Matsalar man fetur a Nijar ta samo asali ne daga rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamnatin mulkin soja da kamfanonin mai na kasar Sin, wadanda ke da rinjaye a fannin hakar mai a kasar.

A farkon shekarar 2024, kamfanin na CNPC ya bayar da bashin Dala miliyan 400 ga Nijar da nufin tallafa mata saboda takunkumin tattalin arziki da ECOWAS ta sanya bayan juyin mulki.

Sai dai gwamnatin mulkin soja ta kasa biyan bashin a kan lokaci, lamarin da ya sa suka kakabawa kamfanin SORAZ harajin dala biliyan 80.

Da kamfanin kasar Sin ya ƙi bayar da ƙarin rance, Nijar ta kore jami’ansa daga kasar tare da kwace asusun ajiyarsu, matakin da ya haddasa rushewar ayyukan hakar mai a kasar gaba daya.

Nijar ta nemi taimakon Najeriya

Sakamakon rikicin, matatar mai ta SORAZ, wadda ke samar da kaso mafi tsoka na man fetur a Nijar, ta dakatar da aiki, kuma hakan ya haddasa matsanancin karancin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

Biyan haraji: Majalisa ta yi wa sojoji gata, an gabatar da muhimmin kudiri a gabanta

Duk da ƙin amincewa da matsalar a fili, gwamnatin Nijar ta gaza shawo kan lamarin, har ta kai ga tilas ta nemi taimakon Najeriya domin shawo kan matsalar.

Wata majiya ta ce ba tare da wata sanarwa ta hukuma ba, gwamnatin Nijar ta tura ministan man fetur da wasu manyan jami’ai zuwa Abuja domin rokon Najeriya ta tallafa mata da gaggawa.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Najeriya ta nuna halin kwarai

Duk da rikicin diflomasiyya da Nijar ta shiga da Najeriya, gwamnatin Najeriya ta amince da bayar da tallafi ta hanyar aikawa da motocin mai 300 zuwa Nijar domin rage radadin matsalar.

Wannan mataki ya kara jaddada matsayin Najeriya a matsayin babbar jagora a Afrika ta Yamma, wadda ke bai wa kasashen makwabta tallafi duk da sabaninsu a baya.

Najeriya za ta tattauna da Nijar

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bude wata kofa domin tattaunawa da kasar Nijar domin samar da mafita kan sabanin da suka samu.

Kara karanta wannan

'Yar TikTok ta yi wani irin mutuwa mai ban tausayi, an samu gawarta a dakinta

Ministan harkokin wajen Najeriya ne ya bayyana cewa matakin zai kawo sauki ko ma warware rikicin diflomasiya da ke tsakanin kasashen biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng