Magana Ta Girma: Trump zai Binciki Zargin Tallafawa Boko Haram daga Amurka

Magana Ta Girma: Trump zai Binciki Zargin Tallafawa Boko Haram daga Amurka

  • Gwamnatin Amurka za ta binciki tallafin da ta bai wa Najeriya da wasu kasashe domin gano yadda aka yi amfani da su
  • Sanata Scott Perry ne ya yi zargin cewa tallafin USAID na taimakawa kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS
  • Ofishin Amurka a Najeriya ya ce suna da tsarin sa-ido domin tabbatar da cewa tallafin da suke bayarwa ya kai ga inda ya dace

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ta dauki matakin binciken tallafin da ta bai wa kasashe daban-daban, ciki har da Najeriya, domin gano yadda aka yi amfani da su.

Wannan mataki na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya dakatar da duk wani tallafi da Amurka ke bayarwa na tsawon kwanaki 90 tun daga 20 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Rumbun sauki: Gwamna ya bude wuraren sayar da abinci da araha ga talakawa

Trump
Gwamnatin Trump za ta dauki mataki kan zargin amfani da kudin Amurka wajen tallafawa Boko Haram. Hoto: Bayo Onanuga|Donald J. Trump
Asali: Facebook

A cewar rahoton da ofishin Amurka a Najeriya ya wallafa a X, binciken zai mayar da hankali kan tallafin lafiya da hukumar USAID ke bayarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin USAID kan ba Boko Haram tallafi

Dan majalisar Amurka, Scott Perry, ya yi zargin cewa hukumar USAID tana bai wa kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS kudi.

A yayin zaman kwamitin majalisa da aka gudanar a makon da ya gabata, Perry ya ce:

“Shin kun san wa ke amfana da wannan kudin? Kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS.”

Ya ce gwamnatin Amurka na bayar da Dala miliyan 697 a kowace shekara, kuma akwai rahotannin da ke nuna cewa an yi amfani da kudin wajen horar da 'yan ta'adda

Amurka ta jaddada aniyar yaki ta'addanci

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya tabbatar da cewa suna da tsarin sa-ido da ke tabbatar da cewa duk wani tallafin da suke bayarwa ya kai ga inda ya dace.

Kara karanta wannan

An gano dalilin faduwar farashi a shahararriyar kasuwar abinci a Kano

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ofishin jakadancin ya ce:

“Mun tanadi hanyoyin sa-ido domin tabbatar da cewa tallafinmu yana kai wa mutanen da suka dace.
"Mun kuma yi tir ta’addancin Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.”

Haka kuma, sanarwar ta tunatar da cewa tun a ranar 14 ga Nuwamba, 2013, Amurka ta ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa.

Wannan mataki ya hana su samun kudi, shiga Amurka, da gudanar da harkokinsu a kasashen duniya.

Amurka za ta cigaba da aiki a Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka ya tabbatar da cewa suna aiki tare da gwamnatin Najeriya da sauran kasashe domin dakile ayyukan ta’addanci.

Sanarwar ofishin ta ce:

“Gwamnatin Amurka na ci gaba da aiki tare da Najeriya da sauran kasashen yankin domin yaki da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

"Bai dace gwamnati ta nade hannayenta ba": Ndume ya nemi majalisa ta duba zargi kan USAID

A cikin shekaru 15 da suka gabata, Boko Haram ta haddasa barna a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya, inda ta kashe dubban mutane tare da kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula.

Gwamnatin Amurka na kokarin ganin cewa tallafin da take bayarwa bai fada hannun kungiyoyin ta’addanci ba, tare da yin hadin gwiwa da Najeriya domin kawo karshen matsalar.

'Yan Najeriya na buya a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Najeriya da suke Amurka sun bayyana halin da suke ciki bayan gwamnatin Trump ta fara farautar bakin haure.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa sun daina zuwa wuraren aiki da wuraren ibada domin jin tsoron kar hukumomi su kama su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng