Amurka Ta Cafke babban Sarki a Najeriya, Ana Zarginsa da Hannu a Badakalar $4.2m

Amurka Ta Cafke babban Sarki a Najeriya, Ana Zarginsa da Hannu a Badakalar $4.2m

  • Hukumar FBI ta cafke Oba Joseph Oloyede, Sarkin Ipetumodu daga jihar Osun, bisa zargin satar tallafin COVID-19 na dala miliyan 4.2
  • An kama Oba Oloyede a ranar 4 ga Mayu, 2024, bayan an fitar da takardun kama shi, inda yake fuskantar tuhume-tuhume 13 a kotun Amurka
  • FBI ta ce Oba Oloyede ya wawure miliyoyin daloli ta hanyar amfani da takardun karya na kamfanoni shida don samun rancen COVID-19

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Hukumar binciken tarayya ta Amurka (FBI) ta cafke sarkin masarautar Ipetumodu, da ke jihar Osun, Kudu maso Yammacin Najeriya, Oba Joseph Oloyede.

An ruwaito cewa an kama Oba Joseph Oloyede bisa zarginsa da hannu a satar kudaden tallafin COVID-19 wadanda suka kai kusan dala miliyan 4.2.

FBI ta cafke sarkin Osun da ake zargin ya bace a Najeriya
FBI ta cafke sarkin Osun bisa zargin wawure kudaden tallafin Covid-19 a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

FBI ta cafke sarkin Osun da aka ce ya bace

Kara karanta wannan

'Abin ya yi muni': An kashe mutane 6 da magoya bayan APC, PDP suka kacame da fada

Oba Oloyede, wanda aka ce ya bace a Maris din 2024, an same shi a hannun FBI kuma yana fuskantar tuhume-tuhume 13 a kotun kasa da kasa ta Amurka, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FBI ta gabatar da karar ne a ranar 3 ga Afrilun 2024, inda take tuhumarsa da abokin aikinsa, Edward Oluwasanmi, da hadin gwiwa, zamba da safarar kudade.

Takardun shigar da kara na kotun Amurka sun bayyana cewa an kama Oloyede a ranar 4 ga Mayun 024, bayan samun takarardar izinin kama shi.

Sarkin ya nemi tallafin Covid-19 da takardun karya

FBI ta ce Oloyede ya shirya zamba ta hanyar kamfanoni shida, inda ya nemi tallafin kudin COVID-19 don farfado da kamfanonin da ya yi ikirarin suna shirin durkushewa.

A shekarar 2020, gwamnatin Amurka ta gabatar da shirye-shiryen tallafi irin su PPP da EIDL don taimakawa kamfanoni da rancen kudi saboda cutar COVID-19.

Sai dai, binciken ya nuna cewa Oloyede ya ƙirƙiri takardu na karya don samun miliyoyin daloli ba bisa ka’ida ba.

Yadda basaraken ya yi almundahanar miliyoyin daloli

A cewar bayanan FBI, a cikin watan Yunin 2020, Oloyede ya samu tallafin fiye da $100,000 a matsayin rance ga kamfanoni hudu: Available Tax Services, Available Tutors, Available Financial, da Available Transportation.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi magana kan zargin jefawa bayin Allah bam a jihar Katsina

A watan Oktoba 2021, ya sami rancen $500,000 ga kamfanin JO&A da kuma $500,000 ga kamfanin Available Transportation.

Bincike ya nuna cewa Oloyede ya taimaka wa abokan aikinsa wajen samun rance na karya, inda yake karɓar wani kaso daga cikin kudaden.

FBI, IRS-CI da wasu hukumomi suka binciki badakalar

A cewar masu gabatar da kara, tsakanin Afrilu 2020 da Fabrairu 2022, Oloyede da Oluwasanmi sun samu tallafin sama da $4.2 miliyan daga hukumar SBA.

An ruwaito cewa Oloyede ya riƙe $1.7m don kasuwannin sa da ƙarin $1.3m ta hanyar gabatar da takardun karya.

Ana gudanar da binciken a karkashin hadin gwiwar FBI, IRS-CI, da DOT-OIG tare da rundunar dakarun yaki da zamba ta PRAC.

An shafe watanni babu labarin sarkin Ipetumodu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, rashin sanin halin da Basarake Oba Joseph Olugbenga Oloyede ya jefa al'umma cikin damuwa, bayan ya bace tun a Maris din 2024.

Oba Oloyede ya yi alkawarin dawowa kafin ƙarshen Janairu 2025, amma har yanzu ba a gan shi ba, kuma ba a kammala ginin sabuwar fadar da ya rushe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com