Yadda Sabon Tsarin Shige da Ficen Saudiyya zai Shafi Najeriya da Kasashen Afrika
Kasar Saudiyya ta sauya dokokin mallakar biza domin samun izinin shiga da zama a kasar wanda hakan zai shafi Najeriya da wasu kasashen Afrika.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yayin da ake shirye shiryen fara aikin Hajjin shekarar 2025, kasar Saudiyya ta yi sauye sauye da suka shafi izinin shiga garin mai tsarki.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Saudiyya ta takaita izinin shiga da zama a kasar ga baki daga kasashen ketare har 14 a fadin duniya.

Asali: Twitter
A wannan rahoton, mun tattaro muku kasashen Afrika da dokar za ta shafa da kuma karin haske kan yadda dokar za ta shafi matafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen Afrika da dokar ta shafa
Times of India ta rahoto cewa daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2025 Saudiyya ta takaita ba da bizar shiga kasar kai tsaye ga masu ziyarar bide ido, kasuwanci da kuma ziyarar dangi.
A karkashin sabon tsarin, duk wanda ke neman biza zuwa Saudiyya daga Najeriya da wasu ƙasashe 13 za a takaita masa lokacin shiga da zama a kasar.
Matakin zai yi tasiri musamman ga 'yan kasuwa, masu yawon buɗe ido da kuma iyalai da ke da 'yan uwa a Saudiyya, domin dole ne su nemi sabuwar biza a duk lokacin da suke son tafiya.
Kasashen da dokar ta shafa a Afrika sun hada da:
- Najeriya
- Algeria
- Egypt
- Ethiopia
- Morocco
- Sudan
- Tunisia

Asali: Facebook
Dalilan takaita shige da fice a Saudiyya
Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa dalilin canjin shi ne hana amfani da bisa da za ta ba mutum damar shiga kasar a ko da yaushe.
Hukumomin suna ganin hakan zai hana mutum damar aikin Hajji ba tare da izini ba, kuma ana ganin dokar za ta rage matsalar cunkoso a lokutan Hajj.
A shekarar 2024, matsanancin cunkoso da tsananin zafi ya haddasa rasuwar mahajjata sama da 1,200.
Saboda haka, Saudiyya na fatan wannan mataki zai rage yawan waɗanda ke yin aikin Hajji ba tare da izini ba, tare da tabbatar da tsaro da jin daɗin mahajjata.

Asali: Getty Images
Wadanda tsarin Saudiyyan zai fi shafa
Najeriya na daga cikin ƙasashen da sauyin tsarin zai fi shafa, kasancewar ƙasar tana da babbar al’umma da ke yawan ziyartar Saudiyya.
Miliyoyin 'yan Najeriya da sauran kasashen Afrika ne ke tafiya Saudiyya domin kasuwanci, yawon buɗe ido, ibada da ziyartar kabarin Annabi SAW.
Sabon tsarin zai fi tasiri ga:
- 'Yan kasuwa da ke yawan shiga Saudiyya don harkokin kasuwanci.
- Iyalai da ke da ‘yan uwa a ƙasar, domin za su riƙa buƙatar sabuwar biza a duk lokacin da za su tafi
- Masu yawon buɗe ido waɗanda a baya suka fi amfana da damar samun bizar shiga kasar kai tsaye

Asali: Getty Images
Yaushe za a janye dokar?
Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa wannan sauyi na wucin gadi ne, amma ba a bayyana lokacin da za a sake duba lamarin ba.

Kara karanta wannan
"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki
Ana sa ran hukumomin Saudiyya za su yi nazari kan tasirin sabon tsarin kafin ɗaukar mataki na gaba.

Asali: Facebook
Me ya kamata matafiya su yi?
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta shawarci matafiya da su nemi biza tun kafin lokacin tafiyarsu domin gujewa matsaloli.
An kuma gargadi matafiya da su tabbata sun cika sabbin ka'idojin biza domin gujewa takura a filayen jiragen sama.
Duk da wadannan sababbin ƙa’idoji, Saudiyya na cigaba da kokarin jawo masu yawon buɗe ido daga sassan duniya.
Financial Express ta rahoto cewa kasar na da burin jawo 'yan yawon buɗe ido daga Indiya har miliyan 7.5 a kowace shekara nan da 2030.
Sai dai ana fargabar cewa wannan sabon tsarin zai rage yawan tafiya zuwa Saudiyya a watannin farko na 2025.

Asali: Facebook
Jigawa ta yi hadakar noma da Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta yi hadaka da kamfanin Saudiyya domin habaka noman dabino.

Kara karanta wannan
'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa yana fatan hadakar ta kai jihar Jigawa matsayin kasa da ta fi samar da dabino a Najeriya da Afrika baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng