Salwan Momika: An Kashe Baturen da Ya Kona Alkur'ani a Gaban Masallacin Sweden

Salwan Momika: An Kashe Baturen da Ya Kona Alkur'ani a Gaban Masallacin Sweden

  • Rahoto ya nuna cewa an harbe Salwan Momika a Sweden, mutumin da ya haddasa tarzoma bayan ya ƙona Alƙur'ani a shekarar 2023
  • Firaminista na Sweden ya ce akwai yiwuwar kisan na da alaƙa da wasu ƙasashen waje, kuma ana binciken lamarin
  • Kafofin watsa labaran yankin Södertälje, birnin Stockholm, sun yi bayanin yadda 'yan bindiga suka shiga har gida suka kashe Salwan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sweden - An harbe wani matashi da ya haddasa tarzoma bayan kona Alkur'ani a gaban babban masallacin Stockholm har lahira a Sweden.

An kashe Salwan Momika a wani gida da ke Södertälje, birnin Stockholm, a daren ranar Laraba, kamar yadda masu gabatar da bincike suka sanar.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe baturen da ya kona Al-Kur'ani a kasar Sweden
Sweden: 'Yan bindiga sun kashe mutumin da ya kona Al-Kur'ani a gaban masallaci. Hoto: @Salwan_Momika1
Asali: Twitter

An samu tarzoma sosai bayan da Mista Momika ya kona kwafin littafin Alkur'ani a gaban babban Masallacin Stockholm a shekarar 2023, inji rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Barawon da ya sace kayan N500, 000 a masallaci ya shiga hannu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe baturen da ya kona Al-Kur'ani

Rundunar ‘yan sandan Stockholm ta ce an kama mutane biyar bayan an harbe mutumin mai shekara 40 har lahira a daren Laraba.

An kira jami’an tsaro bayan an sami rahoton harbe-harbe a wani gida da ke Hovsjö da misalin karfe 23:11 agogon Sweden (22:11 GMT) a ranar Laraba.

An samu mutumin da ba a bayyana sunansa ba da raunukan harbi, inda aka garzaya da shi asibiti. Daga baya aka tabbatar da mutuwarsa da safiyar Alhamis.

An kashe Momika yana tsaka da gabatar da shiri

Kafofin yada labarai na yankin sun ce Mista Momika yana tsaka da watsa shirye-shirye kai tsaye a kafafen sada zumunta lokacin da aka harbe shi.

A watan Agusta, aka tuhumi Mista Momika, Ba’Iraqi da ke zaune a Sweden da 'haddasa kiyayya kan wata kabila' a lokacin bazarar 2023.

An ce an shirya yanke masa hukunci kan tuhumar da ake yi masa a ranar Alhamis, amma kotun Stockholm ta dage hukuncin bayan tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Firaministan Sweden, Ulf Kristersson, ya ce hukumomin tsaron kasar suna binciken lamarin saboda akwai yiwuwar yana da alaka da wasu kasashen waje, kamar yadda SVT ta ruwaito.

Kona Al-Kur'ani ya jawo tarzoma a kasashe

An rahoto cewa Mista Momika ya shirya wasu zanga-zangar adawa da addinin Musulunci, wanda ya haddasa fushi a kasashen da Musulmi suka fi rinjaye.

An yi tarzoma a ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza sau biyu, sannan gwamnatin Iraqi ta kori jakadan Sweden daga kasar.

‘Yan sandan Sweden sun ba Momika izinin gudanar da zanga-zangar da ya kona littafin Alkur'ani, bisa doka ta ‘yancin fadar albarkacin baki.

Daga baya gwamnatin Sweden ta yi alkawarin nemo hanyoyin shari’a don hana zanga-zangar da ke dauke da kona litattafin mai starki.

Fafaroma ya yi Allah wadai da kona Al-Kur'ani

A wani labarin, mun ruwaito cewa Fafaroma Francis ya yi tir da kona Alƙur’ani mai girma da Salwan Momika da wani abokinsa suka yi a Sweden.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Babban shugaban Kiristan ya jaddada cewa dole ne a girmama duk wani littafi da wasu ke dauka a matsayin mai tsarki kuma suke daraja shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel