Trump Ya Kafawa Saudiyya Ƙahon Zuƙa, An Ji Abin da Ya Jawo Faɗuwar Farashin Mai
- Farashin mai ya fadi bayan Donald Trump ya kafawa kasar Saudiyya da kungiyar OPEC kahon zuka na su rage farashin man
- Sabon shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa zai sanya sababbin haraji kan Rasha, Tarayyar Turai, Kanada, Mexico da China
- Masana sun ce raguwar ajiyar danyen mai a Amurka da kuma damuwar sabbin haraji na Amurka na iya rage bukatar mai a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Farashin mai ya fadi da kashi 1% a ranar Alhamis bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya umarci Saudi Arabia da OPEC su rage farashinsa.
Rashin tabbas kan yadda haraji da manufofin makamashi na Trump za su shafi ci gaban tattalin arziki na duniya da bukatar makamashi sun kuma shafi farashin.

Asali: Getty Images
Farashin mai ya fadi a kasuwar duniya
Farashin man Brent ya fadi da kashi 0.9%, zuwa $78.29. Farashin man WTI na Amurka ya fadi da kaso 1.09%, zuwa $74.62, inji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin ya fadi bayan Trump ya kafawa Saudiyya da OPEC kahon zuki a kan su rage farashin mai a wani jawabin da ya yi a taron tattalin arziki na Duniya a Davos, Switzerland.
"Kiran Trump na rage farashin mai zai zama abin murna ga masu kamfanoni, amma masana'antar man Amurka da sauran masu samar da mai na duniya za su yi taka tsantsan."
- Inji Clay Seigle, babban malami a Cibiyar Tsaro da Harkokin Duniya.
An samu raguwar ayyukan mai a Amurka
Masana'antar makamashi na neman karin zuba jari a cikin ayyukan mai da iskar gas na duniya, yayin da ake ganin rage farashin mai na iya jawo damuwa ga masana'antar.
A makon da ya gabata ayyukan danyen mai na Amurka suka ragu sosai, raguwar da ba a gani ba tun daga watan Maris na 2022 , in ji hukumar EIA.
Hukumar EIA ta ce raguwar ayyukan man ta kasance ƙasa da abin da masana suka yi hasashe. Haka nan, ajiyar man da aka tace ya ragu, yayin da farashin ajiyar man fetur ya tashi.
Trump zai sanyawa kasashen duniya haraji
Tasirin tattalin arziki na harajin Amurka na iya rage ci gaban bukatar mai a duniya, in ji Priyanka Sachdeva, babban mai nazari a Phillip Nova.
Trump ya ce zai kara sababbin haraji kan barazanar takunkumin da ya dauka ga Rasha idan kasar ba ta cimma yarjejeniya don kawo karshen yakin Ukraine ba.
Ya kuma yi alkawarin sanya takunkumi kan Tarayyar Turai da kuma sanya haraji na kashi 25% kan Kanada da Mexico da kuma harajin kaso 10% kan China.
Trump ya tsige shugabar sojojin ruwan Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya tsige shugabar sojojin ruwan kasar Adm. Linda Fagan awanni bayan rantsar da shi.
Gwamnatin Trump ta ce ta tsige Fagan saboda ta kasa magance barazanar tsaro a iyakoki, musamman shigo da miyagun kwayoyi da matsalolin cin zarafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng