Dokar Jinsi: Trump Ya Yi Kaca Kaca da Malamar Coci a Taron Masa Addu'a

Dokar Jinsi: Trump Ya Yi Kaca Kaca da Malamar Coci a Taron Masa Addu'a

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nemi limamiyar cocin Washington, Rabaran Mariann Budde ta ba da hakuri kan furucin da ta yi masa
  • Donald Trump ya zargi Rabaran Mariann Budde da tsoma addini cikin siyasa ta hanyar yin kalaman da ya bayyana da cewa ba su dace ba
  • Limamiyar cocin ta bayyana cewa an taru a wajen ibadar ne domin yin addu’a kan hadin kai, ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya nemi afuwa daga limamiyar cocin Washington, Rabaran Mariann Budde.

Rabaran Mariann Budde ta roki Trump ya sauya wasu tsare tsarensa a wani taron addu’a na musamman da aka shirya domin rantsuwar da ya yi ta kama aiki.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Trump
Trump ya yi martani ga malamar coci bayan ta bashi hakuri. Hoto: Chip Somodevilla
Asali: Getty Images

Rahoton AP News ya nuna cewa Rabaran Budde ta yi kira ga Trump ya tausaya wa bakin haure da masu sauya da suke kasar Amurka, wanda hakan ya fusata shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Trump ya bayyana kalaman Budde a matsayin ba su dace ba, inda ya zarge ta da tsoma hannun coci cikin siyasa.

Zargin tsoma coci cikin siyasa

Trump ya zargi limamiyar da yin amfani da taron addu’a domin tsoma addini cikin batutuwan siyasa, yana mai cewa ba ta ambaci cewa wasu bakin haure suna kashe mutane ba.

Ya kuma yi watsi da taron addu’ar, yana mai cewa;

“Wannan taron ba shi da armashi ko ma’ana, kuma bai kayatar ba.”

Donald Trump ya kara da cewa ya kamata Rabaran Budde da cocinta su ba jama’a hakuri saboda kalaman da ta yi.

A lokacin taron, Rabaran Budde ta bayyana cewa an yi addu’ar ne domin neman hadin kai a cikin kasar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko ra’ayi ba.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Rahoton Daily Mail ya tabbatar da cewa Rabaran Budde ta kara da cewa hadin kai ba shi da alaka da jam’iyyar siyasa.

Manufofin Trump kan bakin haure

Taron addu’ar ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ta fitar da sababbin dokoki da suka yi tasiri ga ‘yancin masu sauya jinsi da kuma tsaurara matakan shigowar bakin haure kasar.

Wannan mataki ya jawo martani daga kungiyoyin kare hakkin jama’a, amma Trump ya nace cewa matakan nasa suna da matukar muhimmanci ga tsaron kasa.

Wadanda suka halarci taron addu'ar

Taron addu’ar da aka gudanar a Babban Cocin Kasa na Washington, ya mayar da hankali kan hadin kai da kuma tabbatar da cewa jama’a sun zauna cikin zaman lafiya.

An gayyaci shugabannin addinai daban-daban, ciki har da na addinin Yahudawa, Musulmi, Buddha, da Hindu.

Sai dai an ruwaito cewa shugabannin Kiristoci masu ra’ayin mazan jiya, wadanda ke daga cikin manyan magoya bayan Trump, ba su samu gurbin magana ba.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Duk da haka, wasu daga cikin shugabannin addinan Kirista sun halarci taron, ciki har da Robert Jeffress da Paula White-Cain.

Rabaran Budde ta nemi hadin kai

Budde ta yi amfani da damar wajen yin kira ga Trump da sauran shugabannin kasar su mai da hankali wajen hada kan jama'a, inda ta ce cewa hadin kai shi ne ginshikin cigaban kasa.

Sai dai shugaba Trump ya bayyana kiran nata a matsayin mara amfani, yana mai cewa babu wata manufa mai kyau a kalamanta.

Martanin Bobrisky ga Donald Trump

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen dan daudun Najeriya da aka fi sani da Bobrisky ya yi magana kan dokar da Trump da za ta shafi 'yan daudu.

Bobrisky ya ce ba ya jin tsoron dokar da Donald Trump ya sanya domin shi ya dawo cikakkiyar mace kuma ya shirya bayyana hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng