Wata Ƙasar Afrika Ta Tono Ɗanyen Mai a Karon Farko, Za Ta Goga Kafaɗa da Najeriya

Wata Ƙasar Afrika Ta Tono Ɗanyen Mai a Karon Farko, Za Ta Goga Kafaɗa da Najeriya

  • Rwanda ta sanar da gano danyen mai a karon farko a tafkin Kivu tare da rijiyoyi 13 a iyaka da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo
  • Kasar Rwanda ta bayyana kwarin gwiwa game da yuwuwar gano karin gangunan danyen mai a wani tafki da ke kusa da tafkin Kivu
  • Najeriyar da Angola suna kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afrika, tare da hasashen samar da lita miliyan 3.39 a kowace rana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rwanda - A ranar Laraba, 15 ga Janairu, 2025, Rwanda ta sanar da cewa ta gano danyen mai a karon a tafkin Kivu, tare da rijiyoyi 13 a yankin da ke iyaka da Kongo.

Francis Kamanzi, shugaban hukumar ma'adinai, fetur da gas na Rwanda, ya tabbatar da wannan ci gaba, yana mai cewa abu ne mai kyau cewa ƙasar yanzu tana da mai.

Kara karanta wannan

Abba ya kwato motocin da jami'an gwamnatin Ganduje suka tsere da su a Kano

Kasar Rwanda ta tono danyen mai a karon farko yayin da ta shirya goga kafada da Najeriya
Bayan shekaru da dama na bincike, Rwanda ta sanar da gano danyen mai a karon farko. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Rwanda ta yi nasarar gano danyen mai

Francis Kamanzi ya bayyana cewa an gano rijiyoyi 13 na mai a tafkin Kivu, wanda ke nuna kasancewar mai a yankin, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar samun ƙarin mai, bisa ga manyan rijiyoyin da aka samu a yankin tafkin Great Lakes ta Uganda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Tun fiye da shekaru goma, ƙasar tana gudanar da gwaje-gwaje da bincike a tafkin Kivu da nufin gano danyen mai.

Duk da rikice-rikicen da ke gudana a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Rwanda da Kongo suna tattaunawa kan binciken danyen mai.

Najeriya da Angola ne kan gaba a hako mai

Rahoton Vanguard ya nuna cewa rundunar da Rwanda ke goyon baya sun kama manyan yankuna da ayyukan hakar ma'adanai a yankin, wanda ya jawo rikici.

A halin yanzu, Najeriya da Angola suna kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afirka, tare da hasashen cewa za su jagoranci samar da ganga miliyan 3.39 a kowace rana a bana.

Kara karanta wannan

Bafarawa: Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya fice daga jam'iyyar PDP, ya fadi dalili

Rahoton da aka fitar ya nuna cewa samar da man fetir a Yammacin Afirka zai tashi daga kusan ganga miliyan 6.5 a kowace rana zuwa kusan ganga miliyan 7 kafin ƙarshen 2025.

Rahoton Cibiyar Makamashi ta Afrika (AEC) ya kuma nuna cewa Najeriya da Angola za su samar kusan ganga miliyan 3.7 a kowace rana.

Najeriya za ta jogoranci samar da mai

Ana sa ran cewa nahiyar Afirka za ta ba da gudummawar kusan kashi 8 na man da ake samarwa a duniya a shekarar 2025.

An ce Najeriya ta wuce iyakar samar da mai da aka kayyade mata a Disambar 2024, inda ta hako gangar mai miliyan 1.5 a kowace rana, mafi girma a cikin shekaru hudu.

Ana sa ran Najeriya za ta samar da ganga miliyan 2.06 a kowace rana a shekarar 2025, wanda ya haɗa da man fetir mai haɗi da wanda ba a haɗa ba.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

Farashin mai ya yi tashin gwauron zabi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin fetur nan gaba sakamakon hauhawar farashin man Brent a kasuwannin duniya.

Farashin danyen man Brent yana da matukar tasiri wajen saita farashin mai, inda rahotanni suka nuna cewa farashin gangar Brent ya kai dala $79.76.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.