'Abin Kunya': An Kama Malamin Addini da Matar Aure a Dakin Otel, an Yi Masu Bidiyo
- An yada bidiyon faston cocin Anglican yayin da aka kama shi da wata mata a dakin otel, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a Kenya
- Wasu sun yi imanin cewa tawagar masu daukar bidiyon da matar da mijinta sun tsara yiwa faston bidiyon ne domin neman kudi
- Cocin Anglican a Kenya ta kaddamar da bincike kan zargin, yayin da mutane ke tattauna batun ta hanyar taken #PantsDown
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kenya - Hoton bidiyon wani fasto da aka kama tare da wata mata a dakin otal ya haifar da cece-kuce a Kenya.
Amma wa ke da alhakin watsa wannan bidiyon, da ma wasu makamantansa da dama?
An kama fasto tare da matar aure
Rahoton BBC ya yi nuni da cewa bidiyon faston ya yi kama da wani shirin talabijin na Amurka, inda ake bin diddigin ma'aurata da ke lalata da mata ana musu bidiyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nuna bidiyon a wani shirin labarai a Kenya, inda aka ga faston cocin Anglican, Charles Githinji, ba tare da sutura ba a dakin otal tare da wata kyakkyawar budurwa.
Wani mutum, wanda ya ce shi mijin matar ne, ya shigo dakin tare da tawagar masu daukar hoto da bidiyo.
Kenya: Bidiyon faston ya jawo ce-ce-ku-ce
Faston ya rika neman kayansa cikin gaggawa, amma kafin ya samu damar sanya kayan, tawagar masu daukar bidiyon ta titsiye shi.
An dauki bidiyon tare da dora shi a shafin YouTube, inda ya samu masu kallo sama da 250,000, kuma mutanen Kenya sun fara amfani da taken #PantsDown wajen tattaunawa a kansa.
An yi amfani da wanan taken fiye da sau 2,500 a kwanakin nan, kodayake ba duk maganganun ne suka shafi labarin faston ba.
Ana zargin an shiryawa faston gadar zare
Wannan ba shi ne abu na farko ba. An samu bidiyo makamantansu a shafin YouTube, wadanda dukkansu sun nuna fastocin Kenya a irin wannan yanayi.
A batun Githinji, wasu sun yi imanin cewa tawagar masu daukar bidiyon sun hada baki ne domin kamashi dumu dumu, kuma su samu kudi daga bidiyon.
"Wannan tsari ne kawai," in ji Jackson Njeru, wani shahararren mai wallafa labarai a Kenya wanda ya kirkiri shafin Facebook mai suna 'Deadbeat Kenya.'
Bullar tawagar masu daukar bidiyo a Kenya
Jackson ya kara da cewa:
"Da na kalli bidiyon, akwai abubuwa da ba su yi daidai ba. Matar tana dariya, tana murmushi."
Ya yi imanin cewa matar, mijinta da kuma masu daukar bidiyon suna aiki tare - matsayin tawagar da ke kama fastoci da sauran mutane masu fada a ji a irin wannan yanayi.
Ruth Nesoba, wata ‘yar jarida ta BBC a Kenya, ta ce:
"Bayanin da ke fitowa yanzu shi ne an samu wani rukuni na ‘yan daukar bidiyo masu zaman kansu da ke bibiyar irin wadannan labaran."
Cocin Angelican ta soma bincike
Kafofin watsa labarai suna biyan makudan kudi don irin wadannan bidiyo, in ji ta, domin labaran suna jan hankalin masu kallo da yawa.
Ba a bayyana ba ko haduwar Githinji da matar ta faru ne daga soyayya, karuwanci ko kuma dai tawagar ce ta hada baki don kama faston a wannan yanayi.
Amma Nesoba ta ce yada bidiyon faston ba shi ne abin da ya fi muhimmanci ga ‘yan Kenya da dama a yanzu ba.
Ya zuwa yanzu dai an ce Cocin Anglican a Kenya ta kaddamar da bincike na hukuma kan al’amarin.
Kalli bidiyon a kasa:
An kashe fasto a dakin matar aure
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani malamin addini, Bishop Shina Olaribigbe, ya mutu yayin da yake kokarin sasanta wata rigima tsakanin wasu ma’aurata.
An ce mijin matar ne ya fusata bayan ya tarar da malamin a dakin matarsa, inda ya kai masa hari da wuka, tare da soka masa ita har ya mutu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng