Turmi da tabarya: Matar aure ta mutu yayin da Fasto ke lalata da ita a gidansa
- Wata babbar cocin katolika da ke garin Lusaka a kasar Zambia ta dakatar da wani fasto bayan ta kama shi da laifin kwartanci
- Wata matar aure mai suna Monica Maurice ta mutu a gidansa a yayin da yake kanta yana lalata da ita
- Amma kuma faston ya nuna damuwarsa ta yadda aka dakatar da shi duk da kuwa an gano cewa cutar lamoniya matar ke fama da ita
An dakatar da wani faston cocin katolika bayan matar auren da yake lalata da ita ta mutu a gidansa da ke Zambia.
An dakatar da Faston mai suna Abel Malenga a Lusaka da ke Zambia bayan matar auren ta mutu a yayin da yake kanta suna lalata a gidansa.
Matar mai suna Monica Maurice mamba ce a kungiyar matan cocin St Maurice. Ta ce wa mijinta za ta je bikin mutuwa amma ashe ta wuce gidan fasto ne.
'Yan sandan Lusaka sun ce suna bincike a kan mutuwar matar mai shekaru 42 wacce ta mutu a gidan fasto.
Amma kuma, Abel Malenga ya yi bayanin cewa Alec Banda, shugaban cocin, bai yi masa adalci ba.
KU KARANTA: Yadda wata karuwa ta wurgo kwastoma ta tagar otal sanye da kwaroron roba (Bidiyo)
"Ina so in tabbatar muku da cewa komai zai daidaita. Hankali na kwance yake don nasan adalcin Ubangiji zai tabbata. Ban yi fushi ba a kan yadda aka dauka lamarin. Na bar Ubangiji ya wanke ni," faston yace.
Faston ya kara da ikirarin cewa Monica Maurice ta mutu ne a asibiti sakamakon cutar lamoniya kamar yadda binciken likitoci ya nuna.
Kamar yadda yace, "Ubangiji na da hanyoyin wanke ni. Na gode da irin taimako da kara da kuka nuna min. Ta mutu kusan wata daya da ya gabata," yace.
"Komai na tafiya daidai har zuwa lokacin da babban faston cocin mu ya bai wa sauran fastocin takardar dakatar da ni wacce suka yada."
A wani labari na daban, 'yan sandan yankin Asokwa da ke kasar Ghana sun kama wasu karuwai 11 bayan an zargi daya daga cikinsu da laifin turo kwastomanta ta tagar otal a Kumasi.
Lamarin ya faru a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2020 a otal din Anidaso da ke birnin Kumasi a yankin Ashanti. Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutumin.
Wanda ya mutu yana cikin shakrunsa na 30 kuma an zarga turo shi aka yi daga tagar bayan ya je rage zafi a wurin daya daga cikin karuwan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng