Janar Tchiani Ya Komawa Bokaye yayin da Kasar Nijar ke ‘Yar Tsama da Najeriya

Janar Tchiani Ya Komawa Bokaye yayin da Kasar Nijar ke ‘Yar Tsama da Najeriya

  • Kungiyoyin Bokayen sun yi taro da gwamnatin jamhuriyyar Nijar a babban birnin kasar watau Niamey
  • Malaman tsibbun za su bukaci rundunonin aljannunsu su ga bayan masu shiryawa Nijar makarkashiya
  • Janar Abdourahamane Tchiani wanda ya yi juyin mulki yana zargin ana hada-kai da Faransa domin a cuci Nijar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Niger - Shugaban kasar jamhuriyyar Nijar, Abdurrahmane Tchiani ya na neman yadda zai magance matsalolin al’ummarsa.

Ana zargin cewa Janar Abdurrahmane Tchiani wanda ya kifar da gwamnatin farar hula ya yi zama kungiyoyin bokaye a Nijar.

Kasar jamhuriyyar Nijar
Shugaban kasar Nijar, Abdurrahmane Tchiane ya zauna da bokaye a Niamey Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Bokaye sun hadu da shugaban kasar Nijar

Rahoton da aka samu daga tashar DW Hausa sun ce kungiyar bokayen jamhuriyyar Nijar sun hadu da Abdurrahmane Tchiane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bokayen sun sha alwashin yin amfani da rauhanai domin ganin sun yi maganin duk masu yi wa Nijar da mutanenta zagon-kasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

An yi wannan zama wanda ya jawo surutu ne a fadar shugaban kasar Nijar da ke birnin Niamey a ranar Alhamis da ta wuce.

Nijar ta na zargin ana yi mata makarkashiya

Zargin cewa ana hada-kai da wasu kasashen Afrika domin yakar Nijar ya jawo aka shirya wannan zama na musamman a jiya.

Daily Post da ta kawo rahoton ta bayyana cewa sabani tsakanin gwamnatin sojin Nijar da ta tarayyar Najeriya ta na kara kamari.

An bayyana cewa bokayen da aka kira ba su ambaci sunan wata kasa ko shugaba ba.

Janar Abdurrahmane Tchiani a jawabin da ya yi, ya godewa bokayen ganin yadda za su ka kawowa kasar da al’umma dauki.

Abdurrahmane Tchiani ya ji dadin gudumuwarsu, ya na mai cewa makiya sun taso kasar Nijar a gaba a daidai wannan lokaci.

Tara bokaye a Nijar ya jawo surutu

Tuni aka ji sarakuna da mazauna iyakokin kasashen biyu sun karyata ikirarin gwamnatin Nijar na cewa ana yi mata zagon-kasa.

Kara karanta wannan

Rarara ya ba Tchiani kwana 20 ya maida mulkin Nijar ga fararen hula ko ya dauki mataki

Masu bibiyar labarin a dandalin Facebook sun tofa albarkacin bakinsu yayin da ake zargin Faransa da yi wa kasar makarkashiya.

Juyin mulkin Abdourahamane Tchiani a Nijar

An ji labarin yadda Janar Abdourahamane Tchiani ya yi wa 'Yan jahmuriyyar Nijar jawabi a gidajen talabijin da ya kifar da mulki.

Sojojin da su ka hambara Mohammed Bazoum sun ce sai bayan shekaru za a shirya zabuka kuma da alama haka zancen yake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng