Tirkashi: Wani Ɗan Sanda Ya Sha Giya Ya Bugu, Ya Saki Masu Laifi 13 da Aka Tsare

Tirkashi: Wani Ɗan Sanda Ya Sha Giya Ya Bugu, Ya Saki Masu Laifi 13 da Aka Tsare

  • Wani bugaggen jami'in dan sanda a Zambia ya saki masu laifi 13 daga ofishin hukumar don su je su yi murnar sabuwar shekara
  • Jami'in mai suna Sifeta Titus Phiri ya saki masu laifin a halin maye yana mai cewa suna da 'yancin su yi murnar sabuwar shekara
  • Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Dickson Jere, ya tuna da wani lamari mai kama da wannan da ya faru a 1997

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zambia - Wani jami'in dan sanda da ya sha giya ya bugu a Zambia ya saki masu laifi 13 daga dakin da aka tsare su domin su tafi suyi murnar sabuwar shekara.

An ce an kama jami'in mai suna Sifeta Titus Phiri bayan ya saki masu laifi daga ofishin 'yan sanda na Leonard Cheelo a Lusaka, babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Yan sanda 140 sun mutu saboda hawan jini, an gano sauran dalilan mutuwarsu

Rundunar 'yan sandan Zambia ta kama jami'inta da ya saki masu laifi da aka tsare
Wani dan sandan Zambia ya saki masu laifi 13 da aka tsare bayan ya sha giya ya bugu. Hoto: @znbctoday
Asali: Twitter

Dan sanda ya saki masu laifi da aka tsare

Rahoton BBC ya nuna cewa an tsare wadanda dan sanda ya saki ne a kan zargin aikata laifuka kamar cin zarafin mutane, satar kaya da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, wadanda aka sakin sun fantsama cikin gari yayin da rundunar 'yan sandan kasar da sauran jami'an tsaro suka bazama nemansu.

Mai magana da yawun 'yan sanda, Rae Hamoonga, ya bayyana cewa Phiri, "a cikin yanayi na mayen giya, ya karbe mabuɗan dakin masu laifin daga Constable Serah Banda."

"Yana a halin maye ya sake su" - Kakakin 'yan sanda

Ya ci gaba da cewa:

"Bayan karbe makullan, Sifeta Phiri ya bude dakunan masu laifin na maza da mata, tare da umartarsu tashi, yana cewa suna da 'yancin fita domin murnar sabuwar shekara."
"Daga cikin masu laifin 15 da aka tsare, 13 sun tsere. Bayan wannan lamari, jami'in 'dan sandan shi ma ya tsere daga ofishin."

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Mista Phiri dai bai yi wani bayani game da zargin da ake masa ba tukunna.

Tsohon kakakin shugaban kasa ya magantu

Yayin da yake martani ga wannan lamarin, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa kuma lauya, Dickson Jere ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Ina dariya kowane lokaci na tuna wannan lamari – abin dariya!"
"Amma sai na tuna wani lamari mai kama da wannan da ya taba faruwa a shekarar 1997.
"A cikin daren sabuwar shekarar 1997, marigayi, alkalin kotun koli, Kabazo Chanda, ya umarci a saki masu laifi 53, wasu daga cikinsu suna da hatsarin gaske ga 'yan sanda.
"Mr. Chanda ya fusata saboda an kama masu laifin tun a shekarar 1992, amma har yanzu ba a gabatar da su a gaban kotu ba."

Mista Dickson Jere ya ce lallai akwai matsala sosai idan ana jinkirta yankewa masu laifi hukunci ko danne hannu a gabatar da wadanda ake zargi a kotu.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Malamin addini ya sa bindiga ya harbe wani yaro har lahira

'Yan bindiga sun saki masu laifi a Imo

A wani labarin kuwa, Legit Hausa ta rahoto cewa wasu gungun 'yan bindiga sun farmaki wani ofishin 'yan sanda a Imo, suka kubutar da masu laifi.

An ce 'yan bindigar sun yi amfani da bama bamai wajen farmakar hedikwatar ‘yan sandan da ke a karamar hukumar Ideato ta Kudu a jihar Imo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.