Mahamudu Bawumia: Musulmi Yana Neman Zama Shugaban Kasa a Ghana a Karon Farko
- A safiyar yau Asabar mutane suke fitowa domin kada kuri’arsu ga wanda zai karbi mulki a kasar Ghana
- An fi ganin cewa a tsakanin Mahamudu Bawumia da John Dramani Mahama za a samu wanda zai yi nasara
- Idan mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya yi nasara, musulmi sun samu mulki a karon farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ghana - Mutanen kasar Ghana su na can wajen zaben wanda zai zama sabon shugaban kasar da za a rantsar a Junairun 2025.
Bayan kujerar shugaban kasa, al’umma sun yi layi domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar tarayya 276 a garuruwan kasar Afrikar.
Musulmai a takarar shugaban kasar Ghana
Rahoton BBC ya yi bayanin yadda manyan ‘yan takaran da ake da su a Ghana suke harin kujerar da Nana Akufo-Addo zai bari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar NPP mai mulki ta tsaida musulmi ne; Mahamudu Bawumia wanda yanzu haka shi ne mataimakin shugaban kasa a Ghana.
Tun da Ghana ta samu ‘yanci a watan Maris a shekarar 1957, musulmai bai taba rike mulkin kasar.
Aljazeera a wani rahoto ta ce kiristoci sun zarce 71% na adadin al’ummar Ghana, kasar da ta yi fice wajen mulki farar hula a nahiyar.
Mahama ya kuma neman mulkin Ghana
A gefe guda akwai tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama wanda ya sake tsayawa wannan karo domin jama’a su zabe shi.
John Dramani Mahama da yake rike da tutar NDC, ya yi mulki daga 2014 zuwa farkon 2017, Nana Akufo-Addo ya hana shi yin tazarce.
Mahama zai so ya bar tarihin zama shugaban kasar da ya rasa mulki kuma ya koma ofis kamar yadda Donald Trump ya yi a Amurka.
Nasarar Bawumia kuma kamar yadda The Cable ta ruwaito, ta na nufin jam’iyyar NPP mai-ci ta lashe babban zaben Ghana sau uku a jere.
Mutane 12 na neman shugabancin Ghana
Wani abin ban mamaki a zaben wannan karo shi ne duka manyan ‘yan takaran da ake ji da su sun fito ne daga Arewacin kasar Ghana.
Mutane 12 suke neman zama shugaban kasar Afrika ta yammar, amma masu hasashe sun fi ganin nasara a wajen jam'iyyar NPP ko NDC.
Daga cikin ‘yan takarar akwai mace guda - Nana Frimpomaa Sarpong Kumankumah (CPP).
Juyin mulkin Yakubu Gowon a Najeriya
Ku na da labari kafin a hambarar da Janar Yakubu Gowon, an sanar da shi cewa sojojinsa su na shirin yin juyin mulki a shekarar 1975.
Lokacin yana Kanal, Joseph Nanven Garba ya taimaka aka ga bayan shugaba Gowon ya na halartar taron kasashen Afrika a Kampala.
Asali: Legit.ng