Ma'adanai: Sojojin Nijar Sun Fatattaki Babban Kamfanin Faransa

Ma'adanai: Sojojin Nijar Sun Fatattaki Babban Kamfanin Faransa

  • Ma'aikatar makamashi ta Faransa, Orano, ta bayyana cewa gwamnatin sojin Nijar ta karɓi ikon wajen hako ma'adanin uranium na ƙasar
  • Wannan ya biyo bayan juyin mulki a watan Yulin bara, inda sojojin suka ce za su sake duba dokokin hakar ma'adanai da kamfanonin waje ke yi
  • Legit ta tattauna da wani jami'in DSS a kan jin matakin da suke dauka na samar da tsaro a Najeriya yayin da aka kulla yarjejeniya da Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Niger Republic - Gwamnatin sojin Nijar ta karɓi ikon ma'adanin uranium na kamfanin Orano, wanda ke daga cikin manyan kamfanonin makamashi na Faransa.

Wannan matakin na zuwa ne bayan tsige gwamnatin dimokraɗiyya a watan Yulin bara, wanda ya kawo sabani tsakanin Faransa da Nijer.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya yarje tare da gayyato kasar Faransa ta tona ma'adanai a Najeriya

abdourahamane tchiani
An kori kamfanin Faransa a Nijar. Hoto: Abdourahamane Tchiani
Asali: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa lamarin zai iya kara kawo sabani da aka fara samun tsakanin sojojin da ke mulkin Nijar da kasar Faransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nijar: Yadda aka fara rikici kan ma'adanai

A watan Yuni, Nijer ta janye izinin kamfanin Orano na hako uranium daga babban ma’adanin ƙasar, lamarin da ya sa kamfanin ya dakatar da ayyukansa.

Kafin wannan, Orano ya fuskanci matsalolin shigo da uranium saboda rufe iyakar Nijer da Benin a kan dalilan tsaro.

Kamfanin ya ce adadin uranium mai nauyin tan 1,150 daga shekarun 2023 da 2024 ya makale a Nijar, wanda darajarsa ta kai kusan dala miliyan 210.

Dalilin hana Faransa ma'adanai a Nijar

Sojojin Nijer sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda aka ba kamfanonin ƙasashen waje lasisin hako ma'adanai.

Ministan ma'adanai na Nijar, Kanal Abarchi Ousman ya bayyana cewa rashin amincewar Faransa da gwamnatin sojin ya haifar da ƙaruwar sabani tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

Kanal Abarchi Ousman ya ce bai dace su bar kamfanonin Faransa su ci gaba da hako ma'adanai ba bayan ba su yarda da gwamnatinsu ba.

Ya alakar Nijar da Faransa za ta kasance?

Tun bayan juyin mulki, gwamnatin sojin Nijer na matsawa ƙasashen Yamma, tana neman haɗin gwiwa da ƙasashe kamar Rasha da Turkiyya.

Nijar, wacce ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960, ta kasance tana samar wa Faransa uranium ta hanyar yarjeniyoyi tun kafin juyin mulkin.

RFI ta wallafa cewa kamfanin Orano ya ce zai nemi haƙƙinsa a gaban kotuna, tare da yin kira ga haɗin kai domin dawo da zaman lafiya da ci gaba a harkokin ma'adanin uranium a Nijer.

Legit ta tattauna da jami'in DSS

Wani jami'in DSS da ya bukaci a boye sunansa ya bayyanawa Legit cewa babu abin fargaba a kan alakar da Najeriya ta kulla da Faransa.

Kara karanta wannan

NLC ta janye yajin aiki, gwamna ya amince N80,000 ya zama mafi ƙarancin albashi

Jami'in ya ce akwai matakan tsaro na kasa da kasa da ake dauka kafin kulla irin yarjejeniyar ta inda ba za a samu matsala ba.

Kasar Chadi ta yanke alaka da Faransa

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa kasar Chadi ta sanar da yanke alaƙar soji da kasar Faransa saboda wasu dalilai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ministan harkokin wajen Chadi, Abderaman Koulamallah ne ya tabbatar da lamarin, inda ya ce lokacin rabuwa ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng