Yadda Tinubu Ya Yarje Tare da Gayyato Kasar Faransa ta Tona Ma'adanai a Najeriya
- Gwamnatin Najeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai da kasar Faransa ba da dadewa ba
- Wannan matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda wasu kasashe ke yanke alaka da Faransa kan hakar ma'adanai
- Wannan rahoton ya tattauna kan fa'idar yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da Faransa da kalubalen da ke tattare da hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce, Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kasar Faransa domin inganta hakar ma’adanai.
Wannan matakin na zuwa ne yayin da Jamhuriyar Nijar ta tsuke iyakokin hako ma’adanan uranium din ta daga hannun Faransa.
An wannan rahoton, Legit ta tattaro muku bayanai a kan yadda yarjejeniyar Najeriya da Faransa kan hakar ma'adanai za ta kasance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yarjejeniyar kasar Najeriya da Faransa
A ziyarar aikin da shugaba Tinubu ya kai Faransa a makon da ya wuce, Najeriya da kasar Turan sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da nufin bunkasa hakar ma’adanai.
Ma'aikatar yada labarai ta kasa ta wallafa a Facebook cewa yarjejeniyar ta kunshi:
- Hada kai wajen bincike da hakar ma'adanai
- Musayar dalibai domin ba su horo na musamman
- Rage illa ga muhalli ta hanyar hakar ma’adanai cikin tsafta da bin ka’idoji
Ministan ma’adanai, Dr. Oladele Alake ya bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta kara fito da martabar Najeriya a fannin hakar ma’adanai a duniya.
Faransa: Hakar ma'adai a Najeriya da Nijar
Yayin da Najeriya ke gayyatar Faransa ta shiga harkar ma’adanai, Nijar ta tsame hannun Faransa daga hakar uranium dinta.
Rahoton BBC ya nuna cewa hukumar Orano ta Faransa ta tabbatar da cewa gwamnatin sojan Nijar ta kwace ikon filayen hakar uranium din da kamfaninta ke kula da su.
Wannan lamari ya janyo tasgaro ga Faransa, musamman ganin cewa uranium daga Nijar na da mahimmanci wajen samar da makamashi na nukiliya.
A yayin da wannan ke faruwa, Najeriya ta kulla alakar ma'adanai da Faransa, wanda hakan ya dauki hankalin masu lura da harkokin diplomasiyya.
Rade-radin zuwan Faransa Najeriya a baya
Tun bayan rattaba hannu a kan yarjejeniyar 'yan Najeriya suka fara nuna rashin gamsuwa da kulla alaka da Faransa.
Dama kuma tun kafin hakan, akwai rade radin cewa Faransa za ta kafa sansanin soji a Najeriya bayan korarta daga Nijar da Chadi.
The Cable ta ruwaito cewa dattawan Arewa sun rubuta takarda ga gwamnatin tarayya a lokacin da zancen ya fara daukar hankula.
Sai dai rahoton Premium Times ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta karyata cewa za ta ba Faransa damar kafa sansanin soji a Arewa.
Me ake tsoro kan zuwan Faransa Najeriya?
Duk da cewa yarjejeniyar Faransa za ta iya bunkasa tattalin arzikin Najeriya, akwai masu ganin cewa yana da mahimmanci gwamnati ta yi taka-tsan-tsan.
Tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omkri ya wallafa a Facebook cewa an fara yada jita jitar cewa shugaba Tinubu ya gayyato Faransa Najeriya domin ta yaki Arewa.
Hakan na nuni da cewa akwai fargabar tsaro da mutane ke nunawa a kan zuwan Faransa hakar ma'adanai a Najeriya.
Najeriya za ta ci riba a yarjejeniya da Faransa?
Jaridar the Nation ta wallafa cewa daga cikin fa'idar da za a samu cikin yarjejeniyar akwai cigaba da hako ma'adanai a ramuka kimanin 2,000 da aka yi watsi da su a Najeriya.
Hakan zai karawa Najeriya samun kudin shiga musamman a yanzu da kasar ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Har ila yau, ana hasashen cewa yarjejeniyar za ta daura Najeriya kan turbar samun fasahar zamani wajen hakar ma’adanai masu mahimmanci.
A yanzu haka dai za a zuba ido domin ganin yadda ayyukan hako ma'adanai za su fara gudana bayan yarjejeniyar.
An ladabtar da kamfanin hakar ma'adanai
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Nasarawa ta cigaba da ɗaukan matakai kan masu hako ma'adanai a jihar domin tabbatar da ingancin tsaro.
An ruwaito cewa gwamantin ta dauki matakin gaggawa kan kamfanin Trimadix Geomin Consult Limited da ke aikin ma'adanai Nasarawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng