Gwamna Abba Ya Ziyarci Jami'o'in Indiya, Ya Bayyana Halin da Ya Samu Daliban Kano

Gwamna Abba Ya Ziyarci Jami'o'in Indiya, Ya Bayyana Halin da Ya Samu Daliban Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci jami’o’in Indiya don duba yanayin rayuwar daliban Kano masu karatu a kasar
  • Abba ya tattauna da daliban Kano a jami’o’in Symbiosis, Kalinga, da Swarrnim kuma ya yaba da hazakar su da kyawawan dabi’u
  • Abba ya kuma zagaya harabar jami’ar Symbiosis da asibitin koyarwarta, tare da nazarin yiwuwar kafa makamancin haka a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Indiya - Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da zagaya jami'o'in kasar Indiya domin ganawa da daliban jihar Kano da ke karatu a kasar.

Wannan ziyarar rangadin na daga cikin kokarin Gwamna Abba na sanin halin da daliban Kano ke ciki a makarantu daban daban da suke karatu a Indiya.

Gwamna Abba ya yi magana yayin da ya ziyarci daliban Kano da ke karatu a Indiya
Gwamna Abba ya yaba da hazaka da kyawawan daliban Kano da ke karatu a Indiya. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamna Abba ya ziyarci daliban Kano a Indiya

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar 4 ga watan Disamba, Gwamna Abba ya sanar da cewa ya ziyarci daliban Kano a wasu jami'o'i uku.

Kara karanta wannan

Bayan fafutukar shekaru 22: Kotu ta ba malamin da aka kora a aiki nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar ta Kano ya sanar da cewa:

"A rana ta biyu ta ziyarar rangadi a Indiya, mun gudanar da zaman tattaunawa tare da ɗalibanmu a Jami'o'in Symbiosis, Kalinga da Swarrnim."

Jami'o'in Symbiosis, Kalinga da Swarrnim na daya daga cikin manyan jami'o'in kasar Indiya wadanda suka samu shiga jadawalin QS na manyan jami'o'in duniya na 2025.

Halin da Abba ya samu daliban jihar Kano

Gwamna Abba ya ce tattaunawar da ya yi da daliban ta yi nasara yayin da ya same su cikin yanayi mai kyau da kuma zama dalibai masu hazaka a makarantun.

Mai girma Abba ya ce mahukuntan jami'o'in sun shaida cewa daliban Kano sun yi daban da saura a bangaren karatu kuma suna nuna kyawawan dabi'u.

"Mun kuma yi amfani da wannan damar wajen zagayawa harabar jami’ar Symbiosis da asibitin koyarwar jami'ar domin duba yiwuwar yin irinsa a Kano."

- A cewar Gwamna Abba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnatin Tinubu ta kori ma'aikata masu 'digiri dan kwatano'

"Za mu sake tura dalibai waje" - Abba

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na sake tura daliban Kano zuwa kasashen waje domin karo karatu.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci daliban Kano da ke karatu a jami'ar Sharjah da ke Indiya, a wata ziyarar rangadi da ya kai kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.