Ana Ta Cacar Baki kan Kudurin Gyaran Haraji, Tinubu Ya Dura Kasar Afrika Ta Kudu
- Jirgin Shugaba Bola Tinubu ya sauka birnin Cape Town, kasar Afrika ta Kudu kamar yadda fadarsa ta sanar a ranar Talata
- Shugaba Tinubu ya sanar da cewa ya ziyarci Afrika ta Kudu ne domin halartar taron kungiyar kasashen biyu karo na 11
- Tinubu ya lissafa wasu daga cikin batutuwan da za su tattauna da Shugaba Cyril Ramaphosa da suka hada da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Cape Town - Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da tawagarsa sun dura Cape Town na kasar Afrika ta Kudu a daren ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya shilla Afirka ta Kudu, domin halartar taron kungiyar kasar Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11.
Tinubu ya dura kasar Afrika ta Kudu
Da misalin karfe 5:22 na safiyar ranar Talata, 3 ga Disambar 2024 shugaban kasar ya sanar da isarsa Afrika ta Kudu a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na isa birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, domin halartar taron kungiyar kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11.
"Taron ya zo a kan gaba, inda ya yi daidai da shekaru 25 na tsarin da aka kafa domin karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu"
- Bola Tinubu.
Tinubu ya ce yana fatan jagorantar tattaunawa a taron tare da shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa kan muhimman fannoni daban-daban.
Abubuwan da za a tattauna a zaman Tinubu da Ramaphosa
Manyan batutuwan da Tinubu ya ce za su tattauna a wajen taron sun hada da ciniki da zuba jari, shawarwarin siyasa, harkokin ofishin jakadanci da ci rani.
Sauran batutuwan sun shafi tsaro da haɗin gwiwar samar da tsaron kasashen biyu, harkar banki, makamashi, masana'antu, da kuma zamantakewa.
Shugaba Tinubu ya bayyana Najeriya da Afrika ta Kudu a matsayin kasashen da ke jagorantar tattalin arizi a Afrika, yana mai cewa:
"Dole ne Najeriya da Afirka ta Kudu su ci gaba da cudanya domin tabbatar da ci gaban kasashen biyu da ma kasashen Afrika baki daya."
Tinubu zai je Afrika ta Kudu daga Faransa
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai wuce Afrika ta Kudu ne bayan ya kammala ziyarar aikin da ya kai kasar Faransa.
Bayan taron ministoci a zauren majalisar dokokin Afirka ta Kudu, an tsara babban taron shugabannin kasashen biyu a ranar Talata, 3 ga Disamba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng