Jerin Kasashen da babu Ruwansu da Bikin Kirismeti da Sabuwar Shekara a Duniya

Jerin Kasashen da babu Ruwansu da Bikin Kirismeti da Sabuwar Shekara a Duniya

Kasashe da dama a faɗin duniya na gudanar da biki a ranar, 25 ga watan Disamba domin murnar zagayowar Kirismeti.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Bikin dai lokaci ne na murna da farin ciki ga wasu mabiya addinin Kirista a ƙasashe daban-daban na duniya.

Kasashen da ba su bikin Kirismeti
Akwai kasashen da ba su murnar Kirismeti Hoto: Omer Messinger
Asali: Getty Images

Ƙasashen da ba su bikin Kirismeti

Sai dai, akwai ƙasashe waɗanda ba su gudanar da bikin murnar ranar Kirismeti da sabuwar shekara, cewar rahoton The Week.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan ƙasashen dai ba su yin bikin Kirismeti ne saboda mafi yawan mutanensu, suna bin wasu addinan ne ba Kiristanci ba.

Ƙasashen dai ba su ba da hutu a ranar Kirismeti domin gudanar da bukukuwa.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Afghanistan

Ƙasar Afghanistan ba ta bikin murnar Kirismeti ko ba da hutu domin ranar, saboda addinin musulunci ne addinin mutanen ƙasar.

Kara karanta wannan

"Ba mu son kowa ya kwana da yunwa," Shugaba Tinubu ya shirya wadata abinci a Najeriya

Sai dai, baƙi ƴan ƙasashen waje da tsirarun masu bin addinin Kiristanci a ƙasar, su kan yi bikinsu a keɓe.

2. Bhutan

Ƙasar Bhutan tana bin tsarin addinin Bhudda ne amma akwai ƴan tsirarun masu bin addinin Kiristanci.

Ba a yin bikin murnar Kirismeti a ƙasar amma dai suna da na su bukukuwan da suke gudanarwa, kamar bikin ranar Bodhi.

3. China

A matsayinta na ƙasar da ba a yin addini, China ta taɓa haramta bikin Kirismeti da addinin Kiristanci.

Sai dai a yanzu ana ɗaukar ranar Kirismeti kamar ranar masoya a ƙasar, inda mutane suke zuwa yin sayayya da kallon fina-finai, cewar rahoton Daily Express.

Kusan kaso 1% na mutanen China Kiristoci ne wanda hakan ya sanya ba su da wani iko sosai na yin bikin Kirismeti.

4. Egypt

Mabiya addinin Kirista a ƙasar Egypt ba su yin bikin Kirismeti a watan Disamba, inda ake kiransu da sunan 'Copts.'

Kara karanta wannan

An gano dalilin wasu ƴan Najeriya na baƙin ciki da farfaɗowar Naira

Zuwa ƙarshen watan Nuwamba da farkon Janairu, suna yin azumi sannan a ranar 7 ga watan Janairu, su yi murnar haihuwar Yesu Almasihu.

5. Mongolia

Mongolia tana bin tsarin addinin Bhudda inda ake gudanar da bukukuwa da al'adu daban-daban, amma ban da bikin Kirismeti.

Ranar 25 ga watan Disamba, tana zama kamar kowace rana ne a wajensu, ba a damu da kirismeti a hukumance ba.

6. Morocco

Mafi yawan mutanen ƙasar Morocco Musulmai ne. Ba a gudanar da wani biki domin murnar Kirismeti.

7. Pakistan

A ƙasar Pakistan, ranar 25 ga watan Disamba, an ware ta ne a matsayin ranar karrama shugabansu kuma wanda ya kafa ƙasar Muhammad Ali Jinnah.

8. Qatar

Ba a gudanar da bikin Kirismeti a ƙasar Qatar saboda mafi yawan mutanen ƙasar Musulmai ne masu bin addinin musulunci.

Ba a ba da hutu a ranar domin Kirismeti da aka yi a Disamba, amma wasu ma'aikatun suna ba ma'aikatansu damar hakura da zuwa aiki.

Kara karanta wannan

Najeriya da kasashen waje sun fara luguden wuta domin murkushe Lakurawa

9. Thailand

Mafi yawan mutanen ƙasar Thailand suna bin tsarin addinin Bhudda ne kamar wasu kasashen da ke yankin.

Mutanen ƙasar ba su yin bikin Kirismeti ko ba da hutu domin ranar, amma suna yin maraba da sauran addinai.

10. Tunisia

Tunisia tana daga cikin ƙasashen da ba a yin bikin Kirismeti. A wajen mutanen ƙasar, ranar kamar kowace rana ce.

Sai dai, masu zuwa yawon buɗe ido da Kiristocin da ke ƙasar suna yin ƴan bukukuwa a ranar.

Ƙasashen da ba su bikin sabuwar shekara

Sabuwar shekarar miladiyya tana farawa ne daga ranar 1 ga watan Janairu. Sai dai ba kowane ƙasashe ba ne suke amfani da wannan kalandar.

Ga jerin ƙasashen da ba a yin amfani da kalandar miladiyya:

  • Saudi Arabia
  • Iran
  • India
  • Bangaladesh
  • Korea ta Kudu
  • Korea ta Arewa

Musulmai sun taya Kiristoci bikin Kirismeti

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu al'ummar Musulmai a jihar Bauchi sun taya mabiya addinin Kirista murnar bikin Kirismeti na shekarar 2023.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bajinta, sun tsallake cin hancin $17,000 daga hannun 'yan damfara

Mutanen sun ziyarci cocin Yalwan Kagadama da ke Bauchi a ranar Litinin, 25 ga watan Disamban 2023, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng