Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Yi Magana kan Nasarar Trump a Zaben Shugaban Amurka
- Elon Musk ya yi magana kan nasarar Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasan Amurka da aka gudanar a ranar Talata
- Attajirin ya bayyana cewa mutanen kasar Amurka sun ɗauki ragamar kawo canji sun miƙa ta a hannun Donald Trump
- Musk na ɗaya daga cikin masu goyon bayan Donald Trump domin ya yi nasara kan abokiyar hamaƴyarsa Kamala Harris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Amurka - Shahararren attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Elon Musk, ya yi magana kan zaɓen shugaban ƙasan Amurka.
Elon Musk ya bayyana cewa mutanen Amurka sun ɗora fatansu a kan tsohon shugaban ƙasa Donald Trump.
Attajirin ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Elon Musk ya ce kan zaɓen Trump?
Elon Musk ya bayyana cewa zaɓar Donald Trump ya nuna cewa mutanen Amurka na son ganin canji kan yadda ake tafiyar da mulkin ƙasar.
Bayanin attajirin na zuwa ne yayin da ake jiran kammala tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasan wanda aka gudanar a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamban 2024.
Attajirin wanda yana daga cikin na gaba-gaba wajen goyon bayan Trump, ya bayyana cewa mutanen Amurka na son tsohon shugaban ƙasan ya kawo canji a ƙasar.
"Mutanen Amurka sun ba Donald Trump ragamar kawo canji a daren yau"
- Elon Musk
Donald Trump ya yi wa Kamala Harris fintinkau
Donald Trump ya shiga gaban abokiyar hamayyarsa, Kamala Harris a zaɓen shugaban ƙasan Amurka.
Ya zuwa safiyar ranar Laraba, Trump na kan gaba wajen samun ƙuri'un wakilan masu zaɓe, inda ya samu ƙuri'u 248 daga cikin 270 da ake buƙata domin lashe zaɓen shugaban ƙasan.
Amurka: Donald Trump ya yi nasara
A wani labarin kuma, kun ji cewa magoya bayan Donald J. Trump sun fara murna yayin da aka fara fitar da sakamakon zaben shugaban kasa a Amurka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald J. Trump ne a gaba yayin da abokiyar hamayyarsa Kamala Harris ke binsa a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari
Asali: Legit.ng