Mayakan Boko Haram Sun Tsero zuwa Kauyukan Borno, An Gano Kasar da Suka Fito

Mayakan Boko Haram Sun Tsero zuwa Kauyukan Borno, An Gano Kasar da Suka Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun fara kwararowa zuwa kauyukan Borno daga yankin Tafkin Chadi
  • An ce sojojin kasar Chadi sun tsananta hare-hare kan 'yan ta'addan domin daukar fansar jami'ansu da aka kashe makon jiya
  • Majiyoyin tsauro sun shaida cewa 'yan ta’addan sun tsero daga dazuzzukan Gubuwa a jamhuriyar Chadi zuwa Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Mutane sun shiga cikin dimuwa yayin da aka rahoto cewa wasu 'yan ta'addan Boko Haram sun fantsama cikin kauyukan jihar Borno.

An rahoto cewa dakarun Chadi sun tsananta hare-hare a yankin Tafkin Chadi lamarin da ya tilasta mayakan Boko Haram tserowa Borno.

Sojojin Chadi sun tsananta hare-hare a Tafkin Chadi, mayakan Boko Haram sun tsero zuwa Borno
Mayakan Boko Haram sun fantsama kauyukan Borno bayan hare-haren sojojin Chadi. Hoto: DJIMET WICHE / Contributor
Asali: Getty Images

Mayakan Boko Haram sun shiga Borno

Kara karanta wannan

NNPP a Kano: Kusoshin jam'iyya sun fara nuna shakku kan shugabancin Kwankwaso

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna kauyukan Borno sun shiga cikin dimuwa saboda fargabar tashe tashen hankula sakamakon shigowar 'yan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin tsaro na cikin gida sun shaida wa jaridar cewa, ‘yan ta’addan sun tsero daga dazuzzukan Gubuwa a jamhuriyar Chadi.

An kuma shaida cewa akwai 'yan ta'addan da suka samu munanan raunuka daga hare-haren da sojojin Chadi ke kai masu.

Sojojin Chadi na kai harin ramuwar gayya

Tashar VOA ta rahoto cewa sojojin kasar Chadi sun kai hare-haren bisa jagorancin shugaban kasar Mahmat Idris Deby, domin daukar fansar sojojinsu da aka kashe a makon jiya.

“Shugaba Mahmat Deby ne ya jagoranci harin na farko a yankin Chadi a wani samame da ya kira ‘Operation Haskanite’ tare da samun nasarar koro maharan daga mabuyarsu.
"Ya kashe da yawa daga cikin 'yan ta'addan ya kuma kwato manyan makamai, yayin da ragowar 'yan ta'addan suka tsallaka cikin daji a kewayen Najeriya da Nijar."

Kara karanta wannan

An yi artabu: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Arewa

- A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta.

Sojojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin saman Nigeriya ta samu gagarumar nasara kan yan ta'addan Boko Haram a wani hari da suka kaddamar kansu.

An ce sojojin sun yi wa mayakan Boko Haram lugudan wuta ta sama a lokacin da 'yan ta'addan ke tsaka da gudanar da taro a yankin Bula Marwa a Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.