'Wani Abu Ya Samu Jirginsa,' Shettima Ya Fasa Zuwa Taron da Tinubu Ya Turasa Wakilci
- An soke tafiyar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zuwa Samoa domin wakiltar Najeriya a taron CHOGM na 2024
- Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa an soke tafiyar Shettima zuwa Samoa bayan wani 'bakon abu' ya afkawa jirginsa a Amurka
- A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana matakin da Tinubu ya dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya soke tafiyarsa zuwa taron shugabannin kasashen Commonwealth na shekarar 2024 a Samoa.
Shugaba Bola Tinubu ne ya wakilta mataimakin nasa domin ya wakilci kasar a taron kungiyar kasashe 56 da suka samu raino daga Ingila.
Wani abu ya samu jirgin Kashim Shettima
Duk da wannan umarni na Tinubu, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta sanar da cewa an soke tafiyar Shettima zuwa Samoa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An soke tafiyar Shettima zuwa Samoa bayan wani 'bakon abu' ya afkawa jirginsa a lokacin da ya tsaya a filin jirgin sama na JFK a birnin New York na kasar Amurka.
Kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar a jiya, ya bayyana cewa, 'bakon abun' ya lalata gilashin jirgin saman.
Shettima ba zai je taron CHOGM ba
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya dauki matakin gaggawa, ya tura tawagar ministoci domin su wakilici Najeriya a taron na CHOGM da ke gudana a Samoa, birnin Apia.
Jaridar This Day ta kuma ruwaito cewa sanarwar ta ce an fara gyara jigrin mataimakin shugaban kasar da ya samu matsala.
"Wani bakon abu ya lalata gilashin bangaren direbobin jirgin saman.
“Ministan muhalli, Balarabe Abass Lawal ne zai jagoranci tawagar Tinubu ya tura domin ta wakilci Najeriya a taron Commonwealth na 2024 (CHOGM) a Samoa."
- A cewar sanarwar Onanuga.
Tinubu ya tura Shettima taron CHOGM
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen taron CHOGM.
An tsara cewa Kashim Shettima zai haɗu da Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin duniya daga ƙasashe mambobi 56 a taron na kungiyar Commonwealth.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng