Kasar Birtaniya Ta yi Magana kan Buƙatar Raba Najeriya

Kasar Birtaniya Ta yi Magana kan Buƙatar Raba Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan wata bukata da shugaban yan a ware, Sunday Igboho ya nema daga kasar Birtaniya
  • A ranar Lahadi ne shugaban yan a waren ya ce ya tura takarda ga firaministan Birtaniya kan neman ƙirƙiro kasar Yarabawa
  • Gwamnatin kasar Birtaniya ta tabbatar da cewa ta karbi takardar da Sunday Igboho ya rubuta amma ta fadi matsayin wasikar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da bayanin da kasar Birtaniya ta yi kan neman raba Najeriya.

Birtaniya ta ce ba ta cusa kanta a harkokin wasu ƙasashe musamman abin da yake da alaka da yanci.

Kara karanta wannan

"Wahala a Najeriya:" Bankin Duniya ya yabi Tinubu, ya ba Shugaban kasa shawara

Bola Tinubu
Birtaniya ta yi magana kan ware Yarabawa a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa martanin Birtaniya ya biyo bayan magana da ake yi ne a kan wata wasika da Sunday Igboho ya rubuta mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar Sunday Igboho ga Birtaniya

A ranar Lahadi da ta wuce shugaban yan a ware na yankin Yarabawa, Sunday Igboho ya rubuta wasika ga kasar Birtaniya.

Sunday Igboho ya rubuta wasikar ne domin neman a marawa kudirinsa na samar da kasar Yarabawa baya wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Birtaniya ta yi magana kan raba Najeriya

Kasar Birtaniya ta ce ta karbi wasikar Sunday Igboho da ya rubutawa Firaministan kasar a ranar Lahadi.

Sai dai kasar ta ce ta karbi wasikar ne a kan tsarin tattara wasiku da ake da shi ba wai domin amincewa da ra'ayin Sunday Igboho ba.

An ruda mutane kan wasikar Sunday Igboho

Birtaniya ta kara da cewa wasu yan jarida sun ruda mutane kan wasikar da Sunday Igboho ya rubuta mata wajen rashin fito da bayanai dalla dalla.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Tinubu ya tafi Faransa,' gwamnati ta yi wa masu adawa martani

Gwamnatin Turan ta tabbatar da cewa ba ta shiga harkokin da ya shafi wasu ƙasashe musamman abin da ya shafi yanci.

Ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya ce ta bukaci Birtaniya ta yi bayani kan yadda ake yaɗa zancen cewa kasar ta amince da bukatar Sunday Igboho.

Tinubu ya karfafi yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya yi bayani ga yan Najeriya kan matsalolin tattalin arziki da ke fama da su a kasar nan.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya za ta fita daga cikin halin matsi zuwa sauki nan gaba ƙadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng