An yi Sauyi a Masallacin Manzon Allah SAW: An Nada Limamai a Makka da Madina
- Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi sauye sauye a masallatai masu alfarma na Makka da Madina a ranar Alhamis
- Rahotanni sun nuna cewa an nada sababbin limaman dindindin da za su rika jagorantar salla a masallatai masu alfarma
- Sheikh Muhammad Bahraj na cikin waɗanda aka naɗa domin limanci a masallacin Annabi SAW da ke birnin Madina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Hukumomi a kasar Saudiyya sun yi sauye sauye a masallatai masu alfarma na Makkah da Madina.
A yau Alhamis, 30 ga watan Rabiu Auwal 1446, gwamnatin Saudiyya ta fitar da sanarwa kan nada sababbin limamai a kasar.
Legit ta tattaro bayanai kan limaman da aka naɗa ne a cikin wani sako da shafin kasar Saudiyya na Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nada limamai a Makka da Madina
Gwamnatin kasar Saudiyya ta nada sababbin limamai guda hudu a masallatai masu alfarma na kasar.
Sababbin limaman za su cigaba da jan sallah da sauran ayyukan addinin Musulunci a manyan masallatan kasar.
Sunayen sababbin limaman da aka nada a Makka
Gwamnatin Saudiyya ta nada Sheikh Badar Al-Turki a matsayin sabon limamin masallacin Makka mai alfarma.
Haka zalika gwamnatin Saudiyya ta nada Sheikh Waleed Al-Shamsan a matsayin sabon limami a masallacin na harami.
Limanan masallacin Manzon Allah SAW a Madina
Kasar Saudiyya ta nada Sheikh Muhammad Bahraj a matsayin limamin dindindin a masallacin Manzon Allah SAW.
A daya bangaren, an nada Sheikh Abdullah Al-Quraafi a matsayin sabon limamin dindindin a masallacin da ke Madina.
An canza tsare tsaren aikin Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa NAHCON ta sanar da wani tsari da hukumomin ƙasar Saudiyya suka kawo wanda za a fara aiwatarwa a 1446.
Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Usara ta ce daga yanzu ciyarwa da ɗakunan kwanan alhazai sun koma hannun Saudiyya.
An ruwaito cewa Usara ta ce tuni shirye-shiryen hajjin suka yi nisa kuma hukumar ta zauna da wakilan jihohi kan wannan sabon tsari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng