Dan Kano Ya Kirkiri Injin Kashe Sauro daga Nisan 1km, Kasashe Sun Fara Nemansa
- Wani dan Najeriya da ke aikin bincike a Korea ta Kudu ya kirkiri na'urar da za ta iya kamawa tare da kashe sauro daga nisan kilomita 1
- An rahoto cewa na'urar da Dakta AbdulQaadir Maigoro ya kirkira za ta iya gane nau'in sauro cikin dakiku da cutar da ya ke dauke da ita
- Da wannan fasahar, ana sa ran Dakta Maigoro zai taimaka wajen yaki da cutar zazzabin sauro ta 'asymptomatic' da ke lalata kwakwalwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wani dan Najeriya daga jihar Kano mai aikin bincike a kasar Korea ta Kudu, Dakta AbdulQaadir Yusuf Maigoro, ya kirkiri wani inji da zai yi yaki da zazzabin cizon sauro.
An ce Dakta AbdulQaadir Maigoro ya kirkiri injin da zai iya kama sauro da ke nesa da shi da mita 600 har zuwa kilomita 1.
Dan Najeriya ya kirkiri na'ura
Tsohon sakataren yada labaran gwamnatin Neja, Ibraheem Dooba wanda ya hadu da Dakta Maigoro a Korea ta Kudu ya wallafa wannan ci gaban a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibraheem Dooba ya bayyana cewa:
"A kasar Koriya ta Kudu, mun gana da wani dan Najeriya, Dakta AbdulQaadir Yusuf Maigoro, wanda cibiyar bincikensa ke yin aiki kan yaki da zazzabin cizon sauro.
"Na'urarsa na iya kama sauro daga nisan mita 600 zuwa kilomita daya. Na'urar tana fara jawo saurayen cikinta, sannan ta kama su."
Tasirin na'urar ga yaki da cizon sauro
Ibraheem Dooba ya ci gaba da cewa wannan na'urar da Dakta Maigoro ya kirkira tana iya gane nau'ikan saro cikin 'yan dakiku tare da sanin irin cutar da suke dauke da ita.
Da wannan ci gaban, Dooba ya ce Dakta Maigoro da farfesansa na aiki tukuru domin yaki da cutar zazzabin sauro ta 'asymptomatic' da ke lalata jiki da kwakwalwa.
Fasahar dan Najeriya ta shiga duniya
Ibraheem Dooba ya bayyana cewa:
"Tuni tawagarsa (Dakta Maigoro) ta kaddamar da wannan fasaha a kasar Zambiya kuma nan ba da jimawa ba za ta cimma yarjejeniya da kasar Kenya.
"Sai dai shi (Dakta Maigoro) ya na da shirin hadin guiwa da gwamnatin kasarsa Najeriya ta hannun jami'o'i, cibiyoyin bincike da ma'aikatar kiwon lafiya."
Dooba ya ce tuni hadin gwiwar Dakta Maigoro da Zambiya ya sa ’yan Zambiya samun kuɗin tallafin bincike na dubunnan daruruwan dalar Amurka.
Dattijo ya kirkiri risho mai ruwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani dattijo dan Najeriya, Mallam Hadi Usman ya kirkiri risho mai amfani da ruwa, da zummar rage dogaro ga amfani da kalanzir.
Hakazalika, Mallam Hadi Usman ya bayyana cewa baya ga risho mai amfani da ruwa, ya kuma kirkiri jirgi mai saukar ungulu, kuma jirgin ya tashi a jihar Gombe.
Asali: Legit.ng