Amurka ta Kwace Jirgin Shugaban Kasa Ana cikin Rigimar Karbe Jiragen Najeriya a Turai

Amurka ta Kwace Jirgin Shugaban Kasa Ana cikin Rigimar Karbe Jiragen Najeriya a Turai

  • Gwamnatin kasar Amurka ta kwace jirgin saman dalar Amurka miliyan 13 mallakin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
  • An ce Amurka ta je har Jamhuriyar Dominican ta kwato jirgin bisa zargin cewa Venezuela ta karya takunkumin da ta kakaba mata
  • Kwace wannan jirgin na zuwa ne kwanakin kadan bayan da aka kwace jiragen fadar shugaban kasar Najeriya guda uku a kasar waje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Kwanaki bayan kwace wasu jirgen shugaban kasar Najeriya a kasashen waje, ita ma Amurka ta kwace wani jirgin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro.

Amurka ta ce ta kwace jirgin saman na dalar Amurka miliyan 13 da ake zargin an sayo wa Nicolas Maduro bisa zargin ya sabawa wata dokar kasar.

Kara karanta wannan

Ana kukan kara kudin fetur: Gwamnati ta sanar da shirin kara kudin haraji a Najeriya

Amurka ta yi magana bayan kwace jirgin shugaban kasar Venezuela, Nicholas Maduro
Amurka ta kwace jirgin shugaban kasar Venezuela, Nicholas Maduro. Hoto: @OANN
Asali: Twitter

Amurka ta kwace jirgin Maduro

CNN ta rahoto cewa an kama jirgin shugaban kasar Venezuela a Jamhuriyar Dominican a ranar Litinin kuma an kai shi jihar Florida, a cewar ma'aikatar shari'a ta Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwace jirgin shugaban kasar ya kara nuna tabarbarewar alaka tsakanin Amurka da Venezuela, da kuma nuna himmar Amurka a bincikenta kan rashawar gwamnatin Maduro.

"Kwace jirgin shugaban kasar saboda zargin laifuffukan ta'addanci sako ne ga duniya cewa babu wanda ya fi karfin doka, babu wanda zai iya tserewa takunkumin Amurka."

- A cewar wani jami'in gwamnatin Amurka.

Venezuela ta karya dokar Amurka

A wani rahoto na Aljazeera, babban lauyan Amurka, Merrick Garland ya ce an siyi jirgin ba bisa ka'ida ba, inda aka yi amfani da wani kamfanin basaja kuma aka fitar da shi daga Amurka.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnatin Kano ta kama 'hedimasta' da zargin saida kayan makaranta

Irin wannan ma'amala ta keta takunkumin da Washington ta sanya a 2019 wanda ya haramta wa 'yan Amurka cinikayya da wani abu ga masu yin aiki a madadin gwamnatin Maduro.

Hukumomin Amurka sun ce an sayi jirgin ne daga wani kamfani da ke Florida a karshen 2022, kuma wani kamfanin basaja na Caribbean ya saye shi a 2023 domin tsallake takunkumin.

An kwace jiragen Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotu a kasar Faransa ta ba da umarnin kwace jiragen saman fadar shugaban kasar Najeriya guda uku.

An ruwaito cewa kwace jiragen fadar shugaban Najeriya ba ya rasa nasaba da takun sakar da gwamnatin jihar Ogun ke yi da wani kamfanin kasar Sin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.