Kisan Kiyashi: Yadda Maƙabartun Gaza Suka Cika Ana Birne Gawa kan Gawa

Kisan Kiyashi: Yadda Maƙabartun Gaza Suka Cika Ana Birne Gawa kan Gawa

  • Al'ummar Falasɗinawa na cigaba da shiga tashin hankali mai muni yayin da yakin da suke yi da Isra'ila ya ƙi ci ya ƙi cinyewa
  • A ruwaito cewa an samu kashe kashe da dama a baya bayan nan wanda har aka samu ƙarancin wuraren da za a birne gawa
  • Masu aikin birne mutane a maƙabarta sun bayyana abin mamakin da suka gani a wannan karon bayan shafe shekaru suna aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Palestine - Mutane Zirin Gaza da ke Falasɗinu sun shiga tashin hankali yayin da kashe kashe ya yawaita.

Hakan na zuwa ne kasancewar yakin da suke da Isra'ila ya doshi wata 10 ba tare da dauko hanyar karewa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsakiyar shagalin biki, sun tafka mummunar ɓarna

Palastine
Makabartu sun cika a Gaza saboda kisa. Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa masu birne mutane sun sha mamaki kan abubuwan da suka gani da ba su taɓa faruwa a baya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashe kashe a yakin Falasɗinu da Isra'ila

Ma'aikatar lafiyar Gaza ta bayyana cewa sojojin kasar Isra'ila sun kashe mutane sama da 40,005 tun fara yakin a kusan watanni 10 da suka wuce.

Duk da cewa ma'ikatar lafiyar ba ta bayyana nau'in mutanen da aka kashe ba, an ruwaito cewa galibinsu mata ne da ƙananan yara.

Kasar Isra'ila na iƙirarin cewa yan ta'adda take kashewa sai dai kuma wani mai aikin makabarta ya ce sam ba haka lamarin yake ba.

Kashe kashe: Maƙabarta ta cika a Gaza

Ma'aikatan maƙabarta sun bayyana cewa a yanzu haka suna rasa wajen da za su birne mutane sai dai su daura gawa a kan gawar da aka birne.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Wani dan shekara 63 mai suna Barakeh da ya shafe shekaru 28 yana aiki a maƙabarta ya ce bai taba ganin tashin hankali irin na wannan karon ba.

Punch ta wallafa cewa Barakeh ya ce kafin fara yakin bai wuce su bunne gawa biyar ko shida a mako ba amma a yanzu suna birne gawa kamar 200 zuwa 300 a mako.

An kashe Falasdinawa a Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa a wani harin da sojojin Isra’ila suka kai kan jama’a, sun hallaka mutane biyar da aka bayyana su da cewa ‘yan Falasdinu ne.

Kasar Isra’ila na ci gaba da yi wa mazauna yankin Falasdinawa kisan kiyashi tun bayan da fada ta sake barkewa tsakaninsu da Hamas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng