Cutar Kyandar Biri Ta Bulla Congo da Wasu Kasashen Afrika, WHO Ta Fitar da Bidiyo

Cutar Kyandar Biri Ta Bulla Congo da Wasu Kasashen Afrika, WHO Ta Fitar da Bidiyo

  • Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana bullar kwayar cutar mpox a wasu kasashen Afirka
  • Kwamitin IHR ya yi nazarin rahotonnin bullar cutar a gabashin Congo da kasashen makota, yana nuna damuwa kan saurin yaduwar cutar
  • Darektan WHO a Afirka, Dakta Matshidiso Moeti, ya jaddada kokarin da hukumar ke yi tare da hadin gwiwar gwamnatoci kan lamarin a yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, darakta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya ayyana barkewar cutar kyandar biri a wasu kasashen Afrika.

Rahoton Dakta Tedros ya nuna cewa an samu labarin bullar kyandar 'Mpox' a Jamhuriyar Congo da wasu kasashen da ke makwabtaka da ita.

Kara karanta wannan

Arangama tsakanin manoma da makiyaya ta jawo asarar rayuka a Adamawa

Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da bullar sabuwar kwayar cutar kyandar biri a kasashen Afrika
WHO, karkashin jagorancin Dakta Ghebreyesus ta yi magana kan barkewar kyandar biri. Hoto: Fabrice Coffrini/Uma Shankar Sharma
Asali: Getty Images

WHO ta ayyana bullar cutar a Congo da sauran kasashen Afrika a matsayin cutar da ke bukatar daukan matakin gaggawa, kamar yadda rahoton shafin hukumar ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masana sun damu da saurin yaduwar cutar

An ce hukumar WHO ta ayyana hakan ne bayan da ta samu rahoton kwararru daga kwamitin gaggawa na IHR game da yaduwar cutar kyandar biri.

Masana daga kwamitin IHR sun yi bitar bayanai daga WHO da ƙasashen da abin ya shafa, inda suka kammala da cewa saurin yaduwar cutar na nuna babbar barazana ga harkar lafiya.

Rahoton kwamitin ya nuna saurin yaduwar kwayar cutar a gabashin Jamhuriyar Congo da kasashen makota, wanda ya haifar da damuwa game da yiwuwar yada cutar ta duniya.

WHO ta yi maganar magance kyandar biri

Dakta Tedros ya jaddada bukatar gaggawar daukar mataki daga kasashen duniya domin dakile yaduwar cutar ta kyandar biri.

Kara karanta wannan

An gano abin da yarjejeniya tsakanin Najeriya da kasar Equatorial Guinea ta kunsa

"Akwai damuwar sosai kan bullar sabon nau'in cutar kyandar biri, da saurin yaduwarta a gabashin Congo, da kuma rahoton yaduwarta a kasashe makota.
"A bayyane yake cewa ana buƙatar haɗin kai na kasashen duniya domin dakatar da wannan barkewar tare da ceton rayuka."

WHO ta bayyana kokarin yakar cutar

Dakta Matshidiso Moeti, daraktan hukumar ta WHO a Afirka, ya jaddada kokarin da ake yi na yaki da cutar.

Moeti ya ce:

“An riga an fara daukar manyan matakai tare da hadin gwiwar kasashe da gwamnatoci.
"La'akari da saurin yaduwar cutar, muna kara kaimi ta hanyar hadin gwiwar ayyukan kasa da kasa domin tallafawa kasashen da abin ya shafa domin dakile yaduwar."

Duba bidiyon a kasa:

Kyandar biri ta bulla a jihar Bayelsa

A wani labarin, mun ruwaiton cewa an samu bullar wata sabuwar cuta makamanciyar kyanda da aka yi wa lakabi da monkeypox (Cutar kyandar biri) a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

An ruwaito cewa akwai mutane 10 da likita guda wanda suka kamu da wannan cuta kuma an killace su a wani bangare na asibitin koyarwa na Neja Delta dake garin Okolobiri Yenagoa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.