Zanga Zanga Ta Ci Shugabar Kasa, Firayim Minista Ta Tsere da Aka Zagaye Fadar Ta

Zanga Zanga Ta Ci Shugabar Kasa, Firayim Minista Ta Tsere da Aka Zagaye Fadar Ta

  • Yayin da zanga-zanga ta yi kamari a Bangladesh, dubban matasan kasar sun nufi fadar gwamnati da ke Dhaka
  • Sojojin kasar sun bayyana cewa lamarin ya sa dole firaministan kasar, Sheikh Hasina ta ajiye aiki kuma ta gudu
  • Matasa sun tsunduma zanga-zanga kimanin wata guda da ta gabata saboda kin jinin yadda gwamnati ke raba ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Bangladesh - Zanga-zangar da aka shafe wata guda ana gudanarwa a kasar Bangladesh ta haifar da da mai ido ga masu yinta.

Firaminstar kasar, Sheikh Hasina ta ajiye aiki sannan ta gudu bayan akalla jami'an tsaro sun kashe mutane sama da 300.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Bangladesh
Firaminstan Bangladesh ta ajiye aiki bayan zanga-zanga Hoto: Munir Uz Zaman
Asali: Getty Images

Tashar Aljazeera ta wallafa cewa daliban sun fara gudanar da zanga-zanga a kan kin amincewa da yadda gwamnati ke raba ayyuka a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kafa gwamnatin riko a Bangladesh

Rundunar sojojin Bangladesh ta tabbatar da cewa Firaminstar kasar, Sheik Hasina ta ajiye aiki kuma ta gudu, CBS News ta wallafa.

Janar Waker-Uz-Zaman ne ya tabbatar da hakan tare da bayyana cewa yanzu haka za a kafa gwamnatin riko domin ci gaba da gudanar da kasar.

Sheik Hasina ta gudu ne bayan jama'ar kasar da ke zanga-zanga sun yi biris da dokar hana fita da aka sanya, tare da nufar fadar ta da ke Dhaka.

Sojojin Bangladesh za su dawo da zaman lafiya

Rundunar sojojin kasar Bangladesh ta yi ikirarin za ta dawo da zaman lafiya bayan zanga-zanga ta hautsina kasar

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Gwiwar masu zanga zanga ta fara sanyi, jama'a ba su fito a Abuja ba

Rundunar ta yi alkawarin tabbatar an yiwa dukkanin wadanda aka kashe da iyalansu adalci, tare da rokon jama'a su koma gidajensu su bar zanga-zanga.

An cafke masu zanga-zanga a Najeriya

A wani labarin kun ji cewa jami'an tsaro sun tarwatsa wadanda su ka fito ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da manufofin gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.

'Yan Najeriya sun bayyana cewa ba za su lamunci cewa matsin rayuwa da tashin farashi da ke addabar kasar nan ba, wanda su ke ganin laifin manufofin gwamnatin Bola Tinubu ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.