Gabas Ta Tsakiya Ta Rikice Bayan Kashe Shugaban Hamas, Isra’ila Ta Kai Kazamin Hari Beirut

Gabas Ta Tsakiya Ta Rikice Bayan Kashe Shugaban Hamas, Isra’ila Ta Kai Kazamin Hari Beirut

  • Rahotanni da ke fitowa na nuni da cewa kasar Isra'ila ta kara kai mummunan hari zuwa birnin Beirut na kasar Lebanon
  • Hukumomi sun tabbatar cewa harin ya yi mummunar barna ciki har da kashe babban kwamandan kungiyar Hisbullah
  • Harin na zuwa ne bayan bayanai da suka nuna cewa ana zargin Isra'ila da kashe jagoran Hamas, Isma'il Haniyeh a Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Beirut, Lebanon - Rahotanni na nuni da cewa an samu mummunan harin a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Harin na zuwa ne bayan an zargi kasar Isra'ila da kisan wani shugaban Hamas Isma'il Haniyeh a kasar Iran.

Benjamin Netanyahu
Isra'ila ta kai hari Beirut. Hoto: Kent Nishimura
Asali: Getty Images

BBC ta ruwaito cewa kasar Isra'ila ta ta dauki alhakin harin kuma ta bayyana dalilin daukan matakin.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra'ila: Dalilin kai harin 'ramuwar gayya' Beirut

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa kasar Isra'ila ta tabbatar da kai hari kudancin Beirut inda sojojin Iran ke zaman ko-ta-kwana.

Kasar Isra'ila ta bayyana cewa harin na ramakon gayya ne kan harin da Hisbullah ta kai mata a yankin Golan da ya kashe mutane 12 a ranar Asabar da ta wuce.

Isra'ila ta kashe kwamandan Hisbullah

A yayin harin, kasar Isra'ila ta yi ikirarin kashe kwamandan kungiyar Hisbullah mai suna Fuad Shukr.

Sai dai zuwa yanzu kungiyar Hisbullah ba ta fito ta bayyana ko an kashe kwamandan ba kuma an samu rade-radin cewa bai mutu ba.

Martanin firaministan Lebanon

Firaministan Lebanon, Najib Mikati ya yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai birnin Beirut inda ya siffanta shi da zalunci tsantsa.

Bayan maganar kisan Fuad Shukr, rahotanni na nuni da cewa harin ya yi sanadiyyar jikkata fararen hula da dama a Beirut.

Kara karanta wannan

Gwamna APC a Arewa ya tona asirin masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa

Iran ta kai harin gayya Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta kai harin ramuwar gayya kan ƙasar Isra'ila inda ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Rahotanni na nuni da cewa harin na zuwa ne bayan Isra'ila da kai hari kan ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na ƙasar Syria.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng