Barack Obama Ya Fadawa Amurka na Zaba Tsakanin Kamala Harris da Donald Trump

Barack Obama Ya Fadawa Amurka na Zaba Tsakanin Kamala Harris da Donald Trump

  • Barack Obama ya bayyana cewa Kamala Harris yake goyon baya ta zama sabuwar shugabar kasar Amurka
  • Tsohon shugaban na Amurka da mai dakinsa Michelle Obama suna tare da jam’iyyar Democrat a zaben Nuwamba
  • Kamala Harris ta ji dadin goyon bayan iyalin a yayin da ta ke shirin tunkarar Donald Trump da jam’iyyar hamayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Barack Obama ya mika goyon baya ga Kamala Harris ta zama shugabar kasar Amurka a zaben da za a gudanar a bana.

Tsohon shugaban na Amurka ya fitar da jawabi inda ya tabbatar da cewa shi da mai dakinsa za su goyi bayan Misis Kamala Harris.

Obama
Barack Obama yana so Kamala Harris ta doke Donald Trump a Amurka Hoto: www.nytimes.com, www.forbes.com
Asali: UGC

Barack Obama suna tare da Kamala Harris

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Barack Obama ya sanar da haka ne a shafinsa na X, ya ce tun a farkon makon nan suka kira Harris a waya domin mara mata baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A farkon makon, Michelle da ni mu ka kira abokiyarmu, @KamalaHarris."
"Mun fada mata cewa za ta yi kyau da shugabar kasar Amurka, kuma ta na da cikakken goyon bayanmu."
"A daidai wannan muhimmin lokaci a kasarmu, za mu yi duk abin da za mu iya domin ganin tayi nasara a Nuwamba."
"Mu na fatan za ku goyi bayanmu."

- Barack Obama

Kammala Harris ta samu kwarin guiwa

Jawabin hadakar da Obama ya fitar ya nuna su na sa ran magoya bayansu za su goyi bayan mataimakiyar shugaban kasar Amurkar.

Idan jam’iyyar Democrat tayi dace a zaben, Harris za ta bi sahun Joe Biden wajen zama mataimakiyar shugaban da ta mulki Amurka.

Kara karanta wannan

Joe Biden da sauran shugabannin Amurka 6 da suka janye daga takarar neman tazarce

Amurka: Kammala Harris za ta bar tarihi?

NY Times ta ce da farko Obama ya fitar da jawabi yana jinjinawa Biden da ya hakura da takara, amma bai yi wa kowa mubaya’a ba.

A jawabin da ya fitar a yanzu, ya nunawa Amurka inda ya dosa a zaben Nuwamba. Donald Trump yana sa ran sake samun mulkin kasar.

A gefe guda, Kamala Haris ta fitar da jawabi a dandalin X, ta na godiya ga gidan Obama da su ka karfafawa takararta guiwa a Amurka.

An harbi Donald Trump a Amurka

Ana da labari cewa shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan harbin Donald Trump a Amurka lokacin da yake yawon yakin neman zabe.

Tinubu ya nuna damuwa kan harin inda ya ce hakan bai dace a tsarin dimukradiyya ba. Tuni dai ya mike ya cigaba da yawon kamfensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng