Joe Biden da Sauran Shugabannin Amurka 6 da Suka Janye Daga Takarar Neman Tazarce
Siyasar Amurka tana cigaba da daukar hankalin duniya musamman yadda zaben shugaban kasar ke sake karatowa a watan Nuwambar 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tun farko za a kara ne a zaben tsakanin Shugaba Joe Biden da tsohon shugaban kasa, Donald Trump kafin janye takara da Biden ya yi.
Shugabannin Amurka da ba su nemi tazarce ba
Jiga-jigan jam'iyyar Democrat da wasu 'yan Majalisu sun goyi bayan mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris domin ta maye gurbinsa, cewar Britannica.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta leko muku shugabannin Amurka da ba su tsaya takara a karo na biyu ba saboda wasu dalilai.
1. James K. Polk
Polk wanda aka haifa a shekarar 1795 shi ne shugaban kasar Amurka na 11 ya mulki kasar daga shekarar 1845 zuwa 1849, bai zarce ba.
2. James Buchanan
An haifi Buchanan a shekarar 1791 a birnin Pennsylvania wanda shi ne shugaban kasar Amurka na 15 daga shekarar 1857 zuwa 1861.
Buchanan shi ma ya shiga jerin shugabannin Amurka da ba su samu damar tsayawa takara ko kuma neman shugabancin kasar ba.
3. Rutherfird Hayes
An haifi Hayes a birnin Ohio wanda ya kasance shugaban kasar Amurka na 19 inda ya mulki kasar daga shekarar 1877 zuwa 1881.
Hayes ya ki amincewa da sake zabensa a matsayin wanda zai yi takara a jam'iyyar Republican inda ya ce wa'adi daya kawai yake bukata.
4. Theodore Roosevelt
Roosevelt shi ma ya janye daga tsayawa takara a 1908 inda ya sake dawowa a 1912 inda ya yi rashin nasara a zaben da aka gudanar.
Roosevelt wanda ya yi takara a jma'iyyar Republican ya dare shugabancin kasar ne a shekarar 1904 wanda ya kawo sauye-sauye.
5. Calvin Coolidge
Coolidge shi ne shugaban kasar na 30 daga shekarar 1923 zuwa 1929, ya gaji kujerar bayan mutuwar Shugaba Warren Harding.
A shekarar 1928, Coolidge ya tabbatar da aniyarsa na kin sake tsayawa takara inda daga bisani ya rasu bayan shekaru hudu.
6. Lyndon Johnson
Johnson ya dare shugabancin kasar bayan hallaka shugaban kasar, John F. Kennedy a 1963 inda ya karasa sauran wa'adinsa.
Shugaban ya bayyana matakin janyewa daga neman takara a 1968 inda ya bayyana haka a jawabinsa a gidan talabijin na kasar da ya ba kowa mamaki.
7. Joe Biden
Shugaban Amurka na 46 daga shekarar 2020 zuwa yanzu wanda ya janye sake tsayawa takara bayan ce-ce-ku-ce kan lafiyarsa da kuma gazawa a muhawara da Donald Trump.
Bayyana matsayarsa ke da wuya jiga-jigan jam'iyyar Democrat suka nuna goyon baya ga mataimakiyarsa, Kamala Harris domin tsayawa takara.
Kamala Harris ta kafa tarihi a Amurka
Kun ji cewa mataimkaiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta kafa tarihi yayin da take samun goyon bayan domin tsayawa takara.
Kamala Harris ta samu gudunmawar $81m wanda shi ne mafi girma da aka taba samu a cikn awanni 24 kacal a tarihin siyasar Amurka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng