Trump Ya Shiga Matsala, Kamala Harris Ta Kafa Tarihi a Amurka da Biden Ya Janye Takara

Trump Ya Shiga Matsala, Kamala Harris Ta Kafa Tarihi a Amurka da Biden Ya Janye Takara

  • Kwana daya bayan Shugaban Amurka, Joe Biden ya janye daga takarar shugaban kasa, mataimakiyarsa ta kafa tarihi
  • Kamala Harris ta kafa tarihin wacce ta fi samun gudunmawa mai girma a tarihin kamfe na zaben shugaban kasa a Amurka
  • Harris ta samu akalla $81m a cikin awanni 24 kacal inda ta wuce Trump da ya samu fiye da $50m a birnin Nwe York a kamfe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Washington DC, Amurka - Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta kafa tarihi bayan janye takara da Joe Biden ya yi.

Harris ta samu gudunmawar akalla $81m domin tsayawa takarar shugabancin kasa a karshen wannan shekara ta 2024.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Kamala Harris ta kafa tarihi a siyasar Amurka bayan janyewar Biden
Kamala Harris ta samu gudunmawa mafi girma a tarihin siyasar Amurka. Hoto: Drew Hallowell, Bloomberg.
Asali: Getty Images

Amurka: Kamala Harris ta kafa tarihi

Wannan gudunmawa da Kammala Harris ta samu shi ne mafi girma a cikin awanni 24 kacal a tarihin kamfen shugaban kasa a cewar The New York Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaaban kasar, Donald Trump ya taba samun gudunmawar fiye da $50m a birnin New York a cikin awanni 24 kacal.

Har ila yau, Shugaban Biden shi ma ya samu $38m ne kacal a cikin kwanaki hudu bayan gazawa a muhawara da ya yi da Trump, BBC ta tattaro.

Biden ya janye takararsa, an ba Harris

Wannan na zuwa ne baya Biden ya janye takarar shugabancin kasar bayan rashin katabus a muhawara da suka yi da Donald Trump.

Masu fashin baki da dama sun yi ta korafi kan muhawarar da aka yi inda suke ganin Biden ba zai iya tabuka wani abu ba a zabe.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

Hatta jiga-jigan jamiyyar Democrat sun yi ta kiran Biden ya janye daga neman shugabancin kasar ka da ya jawo musu asara.

Daga bisani Biden ya ji korafin da ake ta yi inda ya janye wanda aka ba Harris damar tsayawa nan take domin gwabzawa a zaben.

Trump ya yi magana bayan an harbe shi

Kun ji cewa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana a karon farko bayan harbinsa a wurin kamfe da wani matashi ya yi.

Trump ya ce bai ankara ba kawai ya ji harsashi ya wuce ta saman kunnensa na dama yayin kamfe a birnin Pennsylvania da ke kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.