Esther Walson Jack: Muhimman Abubuwa 6 Kan Sabuwar Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya

Esther Walson Jack: Muhimman Abubuwa 6 Kan Sabuwar Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Didi Esther Walson-Jack a matsayin shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bola Tinubu ya ce nadin Walson-Jack a matsayin shugabar ma'aikatan zai fara aiki ne a ranar 14 ga watan Agustan 2024 da muke ciki.

Abubuwan da baku sani ba game da sabuwar shugabar ma'aikatan Najeriya
Jerin muhimman abubuwa game da shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Esther Walson-Jack Jack. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Esther Walson-Jack.
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa Walson-Jack ta fara aiki ne a jihar Rivers inda ta rike mukamai da dama bayan barin jihar.

Legit Hausa ta binciko muku muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Esther Walson-Jack.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kwarewar aiki

Walson-Jack ta shafe shekaru da dama tana aikin gwamnati wacce ta fara tun a jihar Rivers a matsayin lauya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya Sake ɗauko mace, ya naɗa ta a shirgegen mukami a gwamnatin tarayya

Ta fara aiki a matsayin lauyan gwamnatin jihar a ma'aikatar shari'a kafin ta yi aiki da Gwamnatin Tarayya a bangarori da dama.

2. Farkon ma'aikatan Bayelsa

Bayan ƙirƙirar jihar Bayelsa a shekarar 1996, Walson-Jack na daga cikin farkon ma'aikata a ma'aikatar shari'a.

Ta taka rawa matuka wurin kawo ci gaba a sabuwar hukumar ma'aikatan jihar da aka kafa a lokacin.

3. Kirkirar sababbin dokoki

Walson-Jack ta kirkiri bangare na musamman a jihar Bayelsa da ke gyaran fuska ko samar da sababbin dokoki a jihar.

Ta dauki nauyin dabbaka dokoki da kuma gyara dokokin mulkin soja daga shekarun 1996 zuwa 1999 da kuma dokokin Majalisar daga 1999 zuwa 2002.

4. Mukamai a ma'aikatar Tarayya

Sabuwar shugabar ma'aikatan ta rike mukamai da dama a matakin Gwamnatin Tarayya da ke birnin Abuja.

Walson-Jack ta rike mukamin mataimakiyar darakta a hukumar Neja Delta ta biyu kafin daga bisani ta samu karin girma zuwa mataimakiyar darakta ta daya.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2024 zai karu, shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi a kara tiriliyoyin Naira

5. Kwararriyar mawallafiya

Walson-Jack bayan kasancewa kwararriyar ma'iakaciya a bangarori da dama, ta wallafa littatafai da dama.

6. Mukamin shugabar ma'aikatan Tarayya

Walson-Jack ta samu mukamin shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya wanda zai fara aiki a watan Agustan 2024.

Ta karbi ragamar mukamin daga tsohuwar shugabar ma'aikatan, Folasade Yemi-Esan bayan ta yi ritaya.

Tinubu ya naɗa sabuwar shugabar ma'aikata

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabuwar shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya da ke birnin Abuja.

Tinubu ya naɗa Esther Walson-Jack domin maye gurbin tsohuwar mai rike da mukamin, Folasade Yemi-Esan a jiya Laraba 17 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.