Amurka: FBI Ta Bankado Bayanan Mutumin da Ya Yi Yunkurin Kashe Donald Trump

Amurka: FBI Ta Bankado Bayanan Mutumin da Ya Yi Yunkurin Kashe Donald Trump

  • Hukumar FBI ta bayyana Thomas Matthew Crooks a matsayin wanda ya kai harin kisan gilla kan tsohon shugaban kasar Donald Trump
  • An ce Thomas Crooks, dan shekaru 20 ya kasance dan jam'iyyar Republican ne kamar yadda bayanan kada kuri'arsa suka nuna
  • Kakakin hukumar FBI, Anthony Guglielmi ya ce jami'in leken asirin Amurka ne ya harbe wanda ake zargin bayan kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta bayyana sunan Thomas Matthew Crooks a matsayin wanda ya kai hari a yunkurin kashe tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Donald Trump ya tsallake rijiya da baya a wani yunkuri na kashe da aka yi a wani gangami a jihar Pennsylvania a ranar Asabar, 13 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya mayar da martani bayan an harbe shi a kamfe, an gano maharbin

FBI ta bayyana sunan wanda ake zargi da yunkurin kashe Donald Trump.
An ce wanda ake zargi da farmakar Donald Trump dan jam'iyyar Republican ne. Hoto: James Devaney/GC Images
Asali: Getty Images

FBI ta bankado wanda harbi Trump

Kamar yadda kafar labaran Aljazeera ta ruwaito, matashin da ake zargi da yunkurin kashe Trump, mai shekaru 20 dan jam'iyyar Republican kamar yadda bayanan zabensa suka nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar FBI, Anthony Guglielmi ya ce jami'in leken asirin Amurka ne ya harbe wanda ake zargin a wurin gangamin.

Anthony Guglielmi ya kara da cewa an kashe mutum daya da ke tsaye a kan hanya yayin harbin sannan wasu biyu suka samu munanan raunuka, inji rahoton BBC.

Daga baya jami’ai sun bayyana cewa dukkanin mutanen uku da harin ya shafa maza ne.

Harbin Trump ya shiga tarihin siyasa

Rahoton kafar labaran CNN ya nuna cewa yunkurin kashe Donald Trump, ya buɗe wani sabon babi a cikin labarin tashe-tashen hankulan siyasa na Amurka.

Harin da aka kaiwa tsohon shugaban kasar ‘yan kwanaki kadan kafin ya karbi tikitin takara a Republican, hari ne ga dimokuradiyya da kuma take hakkin Amurkawa na zabar shugabanninsu.

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

Trump ya magantu bayan an farmakesa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ba da cikakken bayani kan yunkurin kashe shi da aka yi a wani gangami a jihar Pensylvania.

"An harbe ni da harsashi wanda ya huda saman kunnena na dama," Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, da karfe 8:42 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.