Jam'iyyar Trump ta lashe zabukan majalisun dokokin Amurka

Jam'iyyar Trump ta lashe zabukan majalisun dokokin Amurka

- Jam’iyyar Republican ta lashe zaben majalisar Wakilai tare da haramtawa Democrat karbe ragamar majalisar Wakilai a zaben Amurka da aka gudanar inda dan takarar Jam’iyyar Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasa

- Republican ta samu rinjayen kujerun Majalisar Dattijai 54, yayin da 46 suka fada hannun ‘yan Democrat

Jam'iyyar Trump ta lashe zabukan majalisun dokokin Amurka
Donald Trump in WWE

A cikin sanarwar da ya fitar Shugaban Republican Reince Priebus ya ce wannan babbar nasara ce ga Jam’iyyar bayan sun lashe kujerar shugaban kasa tare da ci gaba da rike ragamar Majalisar Dattijai.

KU KARANTA KUMA: Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya

Republican ta samu kujeru 239 a Majalisar Wakilai wanda ya ba Jam’iyyar ci gaba da jagoranci a Majalisar na tsawon shekaru shida. Democrat ta samu kujeru 196 ne a zaben.

Sakamakon zaben dai ya sabawa kuri’un jin ra’ayoyin jama’a da dama da kafofin yada labarai suka gudanar.

Rashin lashe Majalisar Dattijai dai baraka ce ga Democrat musamman wajen kokarin toshe wasu sabbin tsare tsaren shugaban kasa Donald Trump.

A wani labarin kuma a zauren majalisar tamu a nan Najeriya, Rahotanni daga majalisar Dattawa sun nuna cewa sanatoci na nazarin yin watsi da sunayen jakadun wucin gadi su 46 da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar masu don neman amincewarsu.

Da yake karin haske kan batun, Mai Magana da yawun Majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce kwamitin majalisar kan Harkokin waje shi ya bayar da shawarar yin watsi da sunayen sakamakon korafe korafe da aka samu.

https://youtu.be/4Hx0Xu2KLSk

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: