Donald Trump Ya Mayar da Martani Bayan an Harbe Shi a Kamfe, an Gano Maharbin
- Jim kadan bayan harbinsa, tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya yi martani kan abin da ya faru yayin kamfe
- Trump ya bayyana cewa maharbin ya kuskure shi ne ta saman kunnensa inda ya ce ya ji karar harsashen a firgice
- Tsohon shugaban kasar ya kuma jajantawa iyalan wanda ya mutu a taron da kuma wani da ya samu mummunan rauni
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Pennsylvania, Amurka - Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi martani bayan harbinsa a taron kamfe.
Trump ya fitar da sanarwa bayan sha da kyar da ya yi yayin kamfe inda wani matashi ya sammace shi.
Donald Trump ya yi martani bayan harbinsa
Tsohon shugaban kasar ya ce harsashin ya kuskuri saman kunnensa lokacin da ya ke tsaka da jawabi yayin kamfen, cewar Sky News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar FBI ta bayyana matashin da ya yi harbin mai suna Thomas Matthew Crooks cewa yana da shekaru 20 kacal a duniya.
Jami'an tsaro sun tabbatar da kaddamar da bincike kan zargin neman hallaka tsohon shugaban kasar Amurka, Al Jazeera ta tattaro.
Donald Trump ya yi godiya ga jami'an tsaro
"Ina jin lokacin da wata irin kara ta rasa kunnena, nan take na ji karar harsashen ta saman kunnena."
"Jini ya zuba da yawa inda a lokacin ne na fahimci abin da ke faruwa yayin da nake jawabi a kamfe."
"Ina mika godiya ga jami'an hukumar DSS na kasar Amurka da sauran jami'an tsaro yadda suka yi gaggawar daukar mataki."
"Mafi muhimmanci, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan wanda ya mutu a lamarin da kuma wanda ya samu mummunan rauni."
- Donald Trump
An harbi Donald Trump a kamfe
Mun kawo labarin cewa wani matashi ya harbi tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin taron kamfe.
Lamarin ya faru ne a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024 yayin da yake jawabi a Pennsylvani a taron kamfen siyasa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben kasar tsakanin Trump da Shugaba Joe Biden na Amurka.
Asali: Legit.ng