Ana dab da zabe: An Harbi Tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump a Wani Taro a Pennsylvania
- An ji harbi a lokacin da ake tsaka da wani taro a Amurka, inda ake fargabar an harbi tsohon shugaban kasa Donald Trump
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasar Amurka nan da dan kankanin lokaci
- Majiya daga Amurka ta bayyana halin da tsohon shugaban kasar ke ciki da kuma matakan da ake dauka na kariya da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Pennsylvania, Amurka - Jami’an tsaro sun yi hanzarin dauke tsohon Shugaban kasan Amurka Donald Trump daga kan dandamali yana tsaka da jawabi bayan jin sautin harbe-harbe a wani taro a Pennsylvania.
An ga Trump a wani bidiyo yana yamutsa fuska kuma ya daga hannu zuwa kunnensa, kafin ya duka yayin da harbin bindiga ya bayyana a wurin.
Jami'an tsaron sun garzaya da shi cikin gaggawa zuwa wata mota da ke jiransa, kamar yadda rahoton BBC ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da Trump ke ciki, inji na kusa dashi
A cikin wata sanarwa, tawagar yakin neman zaben Trump ta fiyar, an ce ya zuwa yanzu dai lafiyar Trump kalau kuma ana duba shi a asibiti, rahoton New York Times.
A cewar sanarwar:
" Trump yana mika godiya ga jami'an tsaro da masu ba da agajin gaggawa bisa hanzarinsu wajen magance wannan mummunan abu."
Lafiyar Trump kalau, inji jami’an sirri
A cikin wata sanarwa, jami’an sirri suka fitar, sun ce Trump yana cikin koshin lafiya kuma an aiwatar da dukkan wasu matakai don kare shi.
Sun kara da cewa, ana gudanar da bincike mai zurfi ya zuwa yanzu haka kuma za a fitar da karin bayani idan ya samu nan gaba.
Wannan lamari dai na zuwa ne daidai lokacin da zaben shugaban kasar Amurka ke gabatowa, lamarin da ka iya daukar hankalin duniya.
Abin da zai faru idan Trump ya rasa zabe
A wani labarin, mai neman takarar shugaban kasa a Amurka, Donald Trump ya bayyana abin da zai faru idan bai ci zaben Nuwamba ba.
Tsohon shugaban kasar ya ce za a zubar da jini da kashe-kashe idan har ba a zabe shi ba a karo na biyu ba a matsayin shugaba Amurka.
Trump ya bayyana haka ne a Ohio yayin kamfe din ɗan takarar sanatan jam'iyyar Republican, Bernie Moreno, cewar France 24.
Asali: Legit.ng